--
Za'a Iya Rage Farashin Man Fetur A Wannan Makon Cewar Dillalan Man Fetur

Za'a Iya Rage Farashin Man Fetur A Wannan Makon Cewar Dillalan Man Fetur

>
Za'a Iya Rage Farashin Man Fetur A Wannan Makon Cewar Dillalan Man Fetur

Za'a iya rage farashin man fetur a Gidajen mai da ‘yan kasuwa Masu zaman kansu ke Gudanar Dasu a wannan makon, Biyo bayan Shigo da PMS da Hukumar NNPC tayi, in ji dillalan Man Fetur.

Kamar yadda Rana24 ta tattaro cewa an samu ƙarin Farashin man Fetur a Gidajen sayar da man da ‘yan kasuwa masu zaman kansu ke Gudanar da su a baya-bayan nan ne Sakamakon ƙarancin Man Fetur da akayi fama Dashi A faɗin ƙasar.

Sai dai masu Gudanar da aikin a bangaren mai sun tabbatar da cewa wasu kayayyaki da kamfanin na NNPC ya shigo da su sun iso Najeriya, Saboda a halin Yanzu wasu Daga cikin su na jigilar kaya a tashoshin Ruwa.

Jami’in hulda da jama’a na Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN, Cif Ukadike Chinedu, Ya bayyana cewa, “Da zarar kayayyakin sun fara kaiwa Gidajen mai, Farashin man fetur zai ragu, Saboda tsadar da akayi a baya-bayan nan ya biyo bayan faɗuwar kayan da ake buƙata.”

Faduwar Farashin dake tafe wani abin maraba ne ga masu amfani da Man Fetur A Najeriya dake kokawa da tsadar rayuwa. Ana sa ran shiga tsakani na NNPCL Akan lokaci zai sauƙaƙa wa Masu ababen hawa nauyi tare da daidaita Kasuwar man Fetur.

Credit / Rana 24 via Facebook 

0 Response to "Za'a Iya Rage Farashin Man Fetur A Wannan Makon Cewar Dillalan Man Fetur"

Post a Comment