--
Zauren Hadiza Gabon bai saɓa da aikin Jarida ba - Dr. Maude Gwadabe

Zauren Hadiza Gabon bai saɓa da aikin Jarida ba - Dr. Maude Gwadabe

>

 Ƙwararren ɗan Jarida Dr. Maude Rabi'u Gwadabe ya yi fashin baƙi kan shirin nan da Jarumar Kannywood Hadiza Gabon Ke gabatarwa a YouTube.

Hakan dai ya biyo bayan cece-kuce da wasu ke yi na cewar shirin ya kauce wa ƙa'ida.

Sai dai Dr. Gwadabe ya ce babu wata ƙa'idar aikin Jarida da shirin nata ya saɓa wa, sai dai ma satar amsa da ya bai wa sauran ƴan Jarida. 

Ya ce maimakon a tsaya kace-nace kamata yayi ƴan Jarida su yi nazari kan shirin na Gabon don su ga abin da za su koya daga cikinsa.

Dr. Maude Gwadabe dai tsohon ma'aikacin Freedom Radio da BBC Hausa ne sannan ya jagoranci buɗe kafafen yaɗa labarai a ciki da wajen Kano.

Yanzu haka shi ne shugaban jaridar Aminiya wato sashen Hausa na Daily Trust.

Sannan tsoho Malami ne a sashen koyon aikin Jarida na jami'ar Bayero da ke Kano.

Cikakken bayani akasa 👇

https://youtu.be/OT5GHy-g7G0

CREDIT. Freedom Radio Nigeria via Facebook search. 


0 Response to "Zauren Hadiza Gabon bai saɓa da aikin Jarida ba - Dr. Maude Gwadabe"

Post a Comment