--
Mahaifina ne ya kai ni kannywood da hannunsa. Aisha A duniya.

Mahaifina ne ya kai ni kannywood da hannunsa. Aisha A duniya.

>

Jaruma Aisha Umar da aka fi sani da Aisha A Duniya ta ce Mahaifinta ne da kansa ya kai ta Kannywood ya danƙata a hannum Jarumi Tijjani Asase.


Aisha ta ce, da farko ta samu tirjiya kafin daga baya Mahaifinta ya fahimce ta ya sahale mata.


Ta ce babban burinta a rayuwa shi ne ta yi suna duk inda ta je a ce ga Aisha, sai kuma ta samu miji ta yi aure.


A wannan makon, ita ce baƙuwar shirinmu na Daga Kannywood.


Jarumar ta kuma yi martani ga masu yiwa ƴan fim kallon marasa tarbiyya.


Ku latsa wannan link da ke ƙasa don kallon cikakken shirin.

👇👇👇


👉https://youtu.be/R_ZaNFjN0Zw


CREDIT 👉Freedom Radio Nigeria. 


0 Response to "Mahaifina ne ya kai ni kannywood da hannunsa. Aisha A duniya. "

Post a Comment