--
Yanzu yanzu :Zaɓen gwamna: An tura ƴansanda dubu 18,748 zuwa Kano

Yanzu yanzu :Zaɓen gwamna: An tura ƴansanda dubu 18,748 zuwa Kano

>
Zaɓen gwamna: An tura ƴansanda dubu 18,748 zuwa Kano


Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta ce kimanin jami’an tsaro dubu 18,748 ne aka baza a fadin jihar domin gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki na ranar 18 ga watan Maris.


Kwamishinan ƴansanda na jihar, Mamman Dauda ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labara na Ƙasa a Talata a Kano.


Ya ce ƴansanda da sauran jami’an tsaro za su samar  da cikakken tsaro a runfunan zabe dub 11,222 da ke mazabu 484 da ke fadin kananan hukumomi 44 na jihar.


Dauda ya ce tuni aka bayar da umarnin gudanar da aikin tsaro ingantacce ga kwamandojin yankin da jami’an ƴansanda na Caji-ofis domin aiwatar wa.


Ya kuma tabbatar da cewa ƴansanda da sauran jami’an tsaro sun shirya tsaf don kare masu kada kuri’a da jami’an INEC a lokacin zabe da kuma bayan zabe.


“Ina ba da tabbacin tsaro kashi 100 cikin 100 ga duk mazauna jihar masu bin doka da oda cewa za su yi zaɓe cikin yanci a ranar 18 ga Maris ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba,” in ji shi.CREDIT 👉👉Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 


0 Response to "Yanzu yanzu :Zaɓen gwamna: An tura ƴansanda dubu 18,748 zuwa Kano"

Post a Comment