--
YANZU-YANZU :Mùn gama shań wahala amma an yí watsi damù an riƙe waɗanda suka zò daga baya - Fati Nijar

YANZU-YANZU :Mùn gama shań wahala amma an yí watsi damù an riƙe waɗanda suka zò daga baya - Fati Nijar

>



WATA SABÙWA: Mùn gama shań wahala amma an yí watsi damù an riƙe waɗanda suka zò daga baya - Fati Nijar




DAGA: Freedom Radio 


Mawaƙiya Fati Nijar ta koka kan yadda tace an musu Kura da shan bugu a batun tallan ƴan siyasa.


A bidiyon da ta wallafa a shafinta na TikTok, ta ce idan mutum bai yi a hankali ba sai ƴan siyasa sun kai shi sun baro shi.


Ta ce, sun sha wahala lungu da saƙo suna tallan wasu ƴan takara amma ta je gidan ɗaya daga ciki an hana ta ganinsa.


Ta ci gaba da cewa, amma kwatsam sai gashi an ajiye su a gefe ana yi da waɗanda suka zo a bayan-bayansu ba su san ma wahalar da suka sha ba.


Jarumar ta kuma ce, a jira ta zata yi hira inda anan ne zata fayyace abubuwa da yawa.


Wasu na ganin wannan ba zai rasa nasaba da dawowar mawaƙi Dauda Kahutu Rarara da jama'arsa tafiyar Ɗan Takarar Gwamnan Kano a APC ba, wanda a baya Jaruma Fati Nijar ta yi suna wajen tallansa.


CREDIT 👉👉Dokin Karfe TV 

0 Response to "YANZU-YANZU :Mùn gama shań wahala amma an yí watsi damù an riƙe waɗanda suka zò daga baya - Fati Nijar"

Post a Comment