--
YANZU-YANZU :Ina da kyakkyawar alaƙa da duk gwamnonin da na yi aiki ƙarƙashin su, in ji Gawuna

YANZU-YANZU :Ina da kyakkyawar alaƙa da duk gwamnonin da na yi aiki ƙarƙashin su, in ji Gawuna

>






Ina da kyakkyawar alaƙa da duk gwamnonin da na yi aiki ƙarƙashin su, in ji Gawuna


Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana cewa ya na da kyakyawar alaƙa da dukkanin gwamnonin da ya yi aiki da su a Kano.


Gawuna ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da shi a wani shiri na gidan talabijin na TVC mai suna “Countdown Nigeria Decides 2023″.


“Ina da kyakkyawar alaƙa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da sauran tsofaffin Gwamnonin da na yi aiki da su a gwamnatocin baya. Sun haɗa da Shekarau da nayi aiki da shi a matsayin shugaban karamar hukuma, da kuma Kwankwaso da nayi masa kwamishina da kuma a yanzu a matsayina na Mataimakin Gwamna Ganduje, duk kuwa da bambancin jam’iyyar siyasa.


 

A wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran sa, Hassan Musa Fagge ya fitar a yau Asabar a Kano, Gawuna ya ƙara da cewa bai yarda a samu gaba ko hatsaniya tsakanin yan siyasa a Kano ba, inda ya ce "kawai kamata yayi mufi fifita jihar kano fiye da son kanmu”.


Dan takarar gwamnan na jam’iyyar APC ya bukaci al’ummar Kano da su yi la’akari da kwarewa da amincin ƴan takara a matsayin ma’auni yayin kada kuri’a.


 “Ina da kwarewar da ake bukata a harkokin mulki wanda ya sanya ni a saman duk sauran ‘yan takarar gwamna” Gawuna ya bayyana”.


 Ya kuma nanata bayar da ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomin jihar idan aka zabe shi a matsayin gwamnan Kano.


CREDIT 👉👉Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "YANZU-YANZU :Ina da kyakkyawar alaƙa da duk gwamnonin da na yi aiki ƙarƙashin su, in ji Gawuna"

Post a Comment