--
YANZU-YANZU :Ƴansanda sun cafke Alhassan Doguwa a filin jirgin saman Aminu Kano

YANZU-YANZU :Ƴansanda sun cafke Alhassan Doguwa a filin jirgin saman Aminu Kano

>


Ƴansanda sun cafke Alhassan Doguwa a filin jirgin saman Aminu Kano


Rundunar ƴansanda ta kama shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa bisa zarginsa da hannu wajen kashe wasu mutane tare da kona sakatariyar jam’iyyar NNPP a yayin zaben da aka kammala.


Rundunar yansandan ta tabbatar da cewa akalla mutane uku ne su ka mutu a lokacin da aka ƙona sakatariyar yakin neman zaben jam’iyyar NNPP da ke Tudunwada.


Mutane biyu ne su ka kone kurmus a rikicin da ya barke yayin tattara sakamakon zaben majalisar wakilai ta Doguwa/Tudunwada, wanda a karshe aka bayyana Doguwa ya lashe zaben.


Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa ƴansandan sun dauki Doguwa ne a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a lokacin da zai hau jirgi zuwa Abuja a yau Talata.


Wannan jarida ta jiyo cewa a yanzu haka Doguwa na can a sashin binciken manyan laifuka na rundunar ƴansanda a Kano.


Wakilin mu ya kira lambar Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa amma ba ta shiga a daidai lokacin haɗa wannan rahoto.

CREDIT /Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "YANZU-YANZU :Ƴansanda sun cafke Alhassan Doguwa a filin jirgin saman Aminu Kano"

Post a Comment