--
Sadiya Haruna ta ce, babu wata makarantar Islamiyya da aka kai ta bayan da Hisbah ta kama ta.

Sadiya Haruna ta ce, babu wata makarantar Islamiyya da aka kai ta bayan da Hisbah ta kama ta.

>

Fitacciyar mai amfani da kafafen sada zumuntar nan Sadiya Haruna ta ce, babu wata makarantar Islamiyya da aka kai ta bayan da Hisbah ta kama ta.


Sadiya ta kuma bayyana yadda rayuwarta ta kasance lokacin da aka ɗaure ta a gidan yari sanadin Social Media.    


Ta kuma ce, cece kucen da ake ganin tana yi a baya, nada alaka da ƙuruciya amma yanzu girma ya samu, ta yi cikakken hankali.


A cewarta yanzu haka akwai malaminta da yake zuwa har gida ya ke karantar da ita addinin Musulunci bisa raɗin kanta, kuma tana fahimtar karatun sosai.


Sadiya ta kuma yi bayani filla-filla kan ƙalubale da nasarorin da ta cimma a kafafen sada zumunta.

Ga cikakkiyar zantawarta 

👇👇👇

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=1863703280661715&id=100000369575785&mibextid=NnVzG8

Source, Nasiru Salisu Zango via Facebook search. 


0 Response to "Sadiya Haruna ta ce, babu wata makarantar Islamiyya da aka kai ta bayan da Hisbah ta kama ta."

Post a Comment