--
Dole a biyani diyyar zalincin da akayi mini

Dole a biyani diyyar zalincin da akayi mini

>Matar da Aisha Buhari ta lakaɗawa duka ta garzaya kotu ta na neman diyyar miliyan 100


Zainab Kassim, tsohuwar mataimakiya ta musamman ga uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari, ta garzaya kotu bisa zargin yin garkuwa da ita da kuma cin zarafinta a fadar shugaban kasa.


Misis Kassim ta yi hidima ga uwargidan shugaban kasa na tsawon shekaru hudu daga watan Yuni 2015 zuwa Satumba 2019.


Daga bisani an naɗa ta a matsayin mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa a ofishin uwargidan shugaban kasa daga Satumba 2019 zuwa Fabrairu 2022, lokacin da aka sallame ta.


A wata sanarwa da lauyanta, ‘Deji Ajare, ya sanyawa hannu, Misis Kassim ta ce jami’an tsaro na farin kaya, SSS ne su ka yi awon-gaba da ita zuwa fadar shugaban kasa, inda uwargidan shugaban kasar ta lakaɗa mata duka.


Ta bukaci a biya ta diyyar Naira miliyan 100 da kuma dawo mata da wayarta ƙirar 20 Ultra da aka kwace mata.


Source, 👇👇

Daily Nigerian Hausa VIA FACEBOOK SEARCH. 

0 Response to "Dole a biyani diyyar zalincin da akayi mini "

Post a Comment