--
 Bola Tinubu na APC ya lashe zaɓe a jihar Ekiti

Bola Tinubu na APC ya lashe zaɓe a jihar Ekiti

>Ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaɓe a Jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya.


Ekiti ta kasance jiha ta farko da ta fara gabatar da sakamakonta na zaben shugaban ƙasar da aka gudana ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu.


Shugaban hukumar zaben, Farfesa Mahmood ya bayar da dama ga babban jami'in haɗa sakamakon zabe a jihar ta Ekiti domin gabatar da sakamakon a zauren tattara sakamakon da ke Abuja


Babban jami’in lura da zaben jihar ta Ekitin ne ya jagoranci gabatar da sakamakon kamar haka:


APC - 201,494


PDP - 89,554


LP - 11,397


NNPP - 264


SDP - 2,011


Sakamakon ya nuna cewa jami'iyyar APC ce ta samu nasara a zaɓen na jihar Ekiti.


Sai dai babban jami'in haɗa sakamakon zaɓen ya ce an soke zaɓe a wasu mazaɓu biyu saboda wasu matsaloli guda biyu da suka haɗar da:


Tangardar na'urar BVAS da kuma samun adadin mutanen da suka kaɗa ƙuri'a a mazaɓar ya zarta adadin mutanen da na'uar BVAS ta tantance


Source /credit BBC Hausa via Facebook search. 
0 Response to " Bola Tinubu na APC ya lashe zaɓe a jihar Ekiti"

Post a Comment