--
Gwamnatin Tarayya za ta mayar da tubabbun ƴan ta'adda 613 cikin al'umma

Gwamnatin Tarayya za ta mayar da tubabbun ƴan ta'adda 613 cikin al'umma

>







Gwamnatin Tarayya za ta mayar da tubabbun ƴan ta'adda 613 cikin al'umma


Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya, CDS, Lucky Irabor, ya ce akalla ƴan ta’adda 613 da suka tuba masu karamin karfi za a mika su ga gwamnatocin jihohin su domin su koma cikin al’umma.


Irabor ya bayyana haka ne a jiya Alhamis a yayin taron masu ruwa da tsaki na Operation Safe Corridor, OPSC karo na biyar a Abuja.


CDS ɗin, wanda ya samu wakilcin babban jami’in horas da jami’an tsaro na kasa, Adeyemi Yekini, ya ce a halin yanzu, tubabbun ƴan ta’addan na ɗaukar horo kan cire musu tsattsauran ra’ayi da kuma canja musu tunani, ƙarƙashin OPSC.


A cewarsa, taron zai tattauna shirin cire tsatstsauran ra'ayi, canja tunani da kuma mayar da tubabbun ƴan ta'addan cikin al'umma.


Irabor ya ƙara da cewa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya kafa kungiyar ta OPSC a watan Satumbar 2015 a matsayin wata dama ga ƴan ta’adda masu son su ajiye makamai su rungumi zaman lafiya.


Ya kara da cewa: “Haka kuma yana da kyau a bayyana cewa bayan kammala shirin, za a baiwa ko wannen su kayan abinci da kuma wasu kayayyakin amfanin kansa, da kuma kayan da zai fara sana'a, daidai da sana’ar da ya koya a lokacin horaswa ta yadda za su kafa kananan sana’o’i kuma su fara sabuwar rayuwa.”


 Irabor ya bukaci gwamnatocin jihohin da ke karbar bakuncin su da su bayar da goyon bayan da ya dace don baiwa tsoffin mayakan damar manta wa da rayuwar ta'addanci.

Credit /Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Gwamnatin Tarayya za ta mayar da tubabbun ƴan ta'adda 613 cikin al'umma"

Post a Comment