--
Zaku Rabu da duk wani, tabo, Datti da kurajen fuska

Zaku Rabu da duk wani, tabo, Datti da kurajen fuska

>

 Image source /credit /Facebook search Shi lemon tsami yana cire duk wani datti da kurajen da suka yi tabo a fuska mutum. To idan ana amfani da lemon tsami, yana cire su sannan kuma yasa fuska tayi kyau.


Yadda ake amfani dashi: A samu lemon tsami a shafe fuska dashi da hannu da duk inda wani tabo yake sai a barshi yayi minti goma zuwa sha biyar, sai a wanke da ruwan sanyi, a goge fuska da jiki da tawul, amma ba guga ake so ayi ba, dan bubbugawa za ayi ya dan tsane ruwa saboda shi guga yana yiwa fata illa. Bayan an tsane ruwan jikin sai a nemi mai me kyau a shafa tun jiki nada dan damshi damshi. Abinda yasa ake son a shafa mai daga zaran an tsane jiki shi ne saboda shi lemon tsami yana da acid wanda yakan sa jiki ya bushe bayan an shafa shi a jiki


πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹πŸ‹

Sirrin Rike Miji

Islamic medical center

+2348037538596

Sirrinrikemiji@gmail


Source /credit /sirrin rike miji on Facebook. 

0 Response to "Zaku Rabu da duk wani, tabo, Datti da kurajen fuska"

Post a Comment