--
Yan Najeriya Sun Yi Allah Wadai Game Da Tasa Keyar Aminu Da Ake Zargi Ya Caccaki Aisha Buhari A Kafar Sadarwa Ta Tiwita Zuwa Gidan Yari,

Yan Najeriya Sun Yi Allah Wadai Game Da Tasa Keyar Aminu Da Ake Zargi Ya Caccaki Aisha Buhari A Kafar Sadarwa Ta Tiwita Zuwa Gidan Yari,

>

 Image Source /credit / Nigeria reporters Hausa Via Facebook. Yan Najeriya Sun Yi Allah Wadai Game Da Tasa Keyar Aminu Da Ake Zargi Ya Caccaki Aisha Buhari A Kafar Sadarwa Ta Tiwita Zuwa Gidan Yari,


Daga Abbakar Aleeyu Anache


Wannan batu na kama matashin mai suna Muhammad Aminu tare da gurfanar da shi a gaban kulliya ya haifar da muhawara mai zafi a kafofin yada labarai da na sada zumunta a Najeriya,


Inda da dama ke ganin an wuce gona da iri wajen daukar hukunci lakada masa duka daga bisani kotu ta bada umurnin a tura shi gidan yari kafin a cigaba da yi masa shari'a,


Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa a Najeriya irinsu Amnesty international su ka yi Allah wadai da matakin kama Muhammad tare da zargin an take masa hakkinsa na bil'adama, 


Na daya dai an ce wannan laifin a jigawa aka yi sannan aka aika jami'an tsaro suka kama yaron suka je su ka kulle shi aka rika jibgar sa wannan ya keta dokar kasa ya keta dokar bil'adama a cewar Auwal Musa Rafsanjani shugaban gudanarwa na kungiyar Amnesty international, 


Bayanai na nuni da cewa uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari ce ta bai wa jami'an tsaro umurnin dauko mata Aminu daga jihar jigawa bayan ya wallafa wasu kalamai a kanta na zargin ta yi rub da cikin da kudin jama'a kalamai da ba su mata dadi ba,


Da ta ke tsokaci kan lamarin Hajiya Naja'atu Muhammad kwamishiniya a hukumar yan sandan kasar ta ce ya kamata a kama uwar gidan shugaban kasar saboda ta keta doka ita kanta,


Source /credit / Nigeria reporters Hausa Via Facebook. 

0 Response to "Yan Najeriya Sun Yi Allah Wadai Game Da Tasa Keyar Aminu Da Ake Zargi Ya Caccaki Aisha Buhari A Kafar Sadarwa Ta Tiwita Zuwa Gidan Yari,"

Post a Comment