GYARAN GASHI GA MATA.
Image Credit /source /sirrin rike miji on Facebook
GYARAN GASHI GA MATA.
Hadi domin samun gashi mai tsawo
Akwai hanyoyi da dama wadanda mata za su bi domin samar da gashin kai mai tsawo. Abu ne mai sauki. Mata da dama na son ganin kansu da gashi mai tsayi kamar na Indiya. Gashi na daya daga cikin ababen da ke dada wa mace kyau, don haka ya kamata mata ku kula da gashinmu sosai.
Wannan hadin da zan rubuto muku na dada wa gashi maiko, wato yana hana gashi karyewa da sanya shi tsayi da laushi. Ina so a san cewa wannan hadin a kan yi shi ne kamar sau biyu a wata. Idan mutum ya kasance mai yin wani hadi ne daban wanda ba wannan ba, bai kamata ba a rika hada wannan salon gyaran gashi da wani daban in ba haka ba, sai aga kwalliya bata biya kudin sabulu ba.
Abubuwan da za a bukata:
🌿 Man Amla.
🌿 Zuma.
🌿 Ruwan dumi.
Hadi
A zuba cokalin amla biyu a roba.
Sannan sai a zuba rabin cokalin zuma a cikin amla.
A sanya cokalin ruwan dumi kamar 2-3.
A juya hadin har sai sun cakudu da juna. A taje gashi kamin a shafa wannan hadin a fatar kai.
A jira na tsawon mintuna 30.
A wanke kai da man wanke gashi (shampoo).
Amfani da man kwa-kwa; man kwa-kwa na sanya gashi laushi da tsayi da kuma santsi. Yana da kyau a rika shafa man a fatar gashin kai a duk lokacin da za ayi kitso ko kuma a rika gauraya shi a cikin man kitso.
Man zaitun; wannan man na da mahimmanci sosai a jiki baki daya. Sannan kuma yana sanya gashi santsi da baki. Yana kuma magance hurhurar gashi da kuma sanya gashi tsayi da baki da sheki da kuma kyau.
SOURCE /CREDIT /SIRRIN RIKE MIJI ON FACEBOOK.
0 Response to "GYARAN GASHI GA MATA."
Post a Comment