--
Ga abinda ya kamata kusani game da batun kama gomnan Cbn Godwin emefele.

Ga abinda ya kamata kusani game da batun kama gomnan Cbn Godwin emefele.

>

 




Rahotannin da ke kara-kaina a wasu kafafen yada labarai na cewa hukumar tsaron farin kaya na shirin kama gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele.


Wata babbar kotu a Abuja babban birnin kasar ta yi watsi da bukatar DSS ta kamawa da tsare Mista Emefiele.


DSS na tuhumar Godwin da laifukan da suka shafi taimakawa ta'addanci, sai dai kotun ta ce hukumar ta koma ta samo ƙwararan hujjoji da shaidu kafin ta sake dawowa gabanta kan batun.

Abin da kotu ta ce game da batun Emefiele

Wani mai suna US Gambarawa shi ne ya shigar da karar a madadin hukumar tsaron farin kaya ta DSS a ranar 7 ga watan Disambar 2022.

Tuhumar mai lamba FHC /ABJ/CS/2255/2022, ta nuna shari'ar tsakanin DSS da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele.


DSS na zargin Godwin Emefiele, da tallafawa ta'addanci da kudade hakan ya sabawa doka ya kuma aikata laifi kan tattalin arziki.


Mai shari'a John Terhemba Tsoho da aka gabatar da karar gaban shi ya yi watsi da ita.


Ya ce DSS ba ta gabatar da wata kwakkwarar shaidar da ta nuna gwamnan CBN din ya aikata laifin ba, sannan kamata ya yi ace shugaba Muhammadu Buhari ya san da batun.


Takardun tuhumar da kotun ta yi watsi da su, da sashen BBC Pigin ya gani, ya nuna alkalin babbar kotun ne ya dauki matakin.


A hukuncin da ya zartar, Alkalin ya yi bayani kan wasu bayanai da aka yi su a dunkule da ya bukaci a warware da yin bayani dalla-dalla, inda aka ambaci Godwin Emefiele ba tare da an fadi mukaminsa na Gwamnan babban bankin Najeriya ba.


Alkali Tsoho ya kara da cewa ''DSS ba su yi gamsasshen bayani kan ko wanda suke kara mai suna Godwin Emefiele gwamnann CBN ne ko kuma wani mutum mai irin sunansa na daban, don haka ana bukatar wannan bayani.


"Mutane za su yi mamaki da rudani ko wanda ake tuhumar Emefiele na CBN ne ko a'a, saboda ana magana ne fa a kan daya daga cikin babban jami'in gwamnatin tarayya.''


Mai Shari'a Tsoho, ya kuma kafe cewa kamata ya yi tuhumar da DSS suka gabatar ta samu rattaba hannun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tun da shi ne ya nada Emefiele mukamin.


''Lamarin ya yi kama da kotun na son fakewa da guzuma ne ta harbi karsana, ta hanyar amfani da kotun wajen lullube abin da suka aikata ba daidai ba da sun san ya sabawa doka kuma ba za a amince da shi ba.


"Wannan dalilin ne ya sanya ba mu amince da karar da suka shigar ba, har sai sun gabatar da kwakkwarar hujja sannan za mu saurare su, amma ayanzu kam mun yi watsi da batun,'' in ji Alkali Tsoho.

SOURCE /CREDIT /BBC Hausa via Facebook search. 


0 Response to "Ga abinda ya kamata kusani game da batun kama gomnan Cbn Godwin emefele. "

Post a Comment