--
Duk Wanda Bai Ji Dadin Hukuncin Da Aka Yi Wa Abduljabbar Ba, To Lallai Ya Tuntubi Imaninsa, Cewar Shèik Sani Rijiyar Lemo

Duk Wanda Bai Ji Dadin Hukuncin Da Aka Yi Wa Abduljabbar Ba, To Lallai Ya Tuntubi Imaninsa, Cewar Shèik Sani Rijiyar Lemo

>

 


Duk Wanda Bai Ji Dadin Hukuncin Da Aka Yi Wa Abduljabbar Ba, To Lallai Ya Tuntubi Imaninsa, Cewar Shèik Sani Rijiyar Lemo


Yau ne Babban Malamin mu Ash Sheikh Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo (O.O.N) Hafizahullah a gurin karatun Tafsir a Masallacin Usman bin Affan dake Gadon Kaya a Kano ya yi bayani mai gamsarwa game da hukuncin da kotu ta yankewa Abduljabbar Kabara.


Farfesa ya yi bitar irin tabargazar da wannan mutumin ya dinga yi da yadda aka titsiye shi a mukabala da kawo shi kotu da aka yi.


Sannan Farfesa ya kawo misalan irin wadanda suka dinga yi wa Annabi (S.A.W.) izgili a tarihi da yadda Ubangiji ya yi maganinsu.


Sannan Farfesa bayan godiyar Ubangiji ya godewa Gwamnatin Kano da yadda ta kawar da kai aka yi shari'a ta gaskiya.


Haka ya godewa Mai Shari'ah Shehin Malami Ibrahim Sarki Yola saboda yadda ya tsaya ya yi shari'ar Allah. Kuma ya godewa tarin Lauyoyin da suka bayar da gudummawa kyauta akan batun.


Kuma ya godewa sauran al'umma da addu'ar da suka dinga yi har zuwa karshen shari'ar sannan ya yi zargin duk wani wanda zai ji babu dadi akan wannan hukuncin lalle ya tuntubi Imaninsa.


Wannan dai shi ne a takaice ragowar bayanan sai ku nema ku saurara Allah Ya yi dadin tsira da aminci ga fiyayyen Halitta Annbai Muhammad da Alayensa da Sahabbansa ya karawa Farfesa lafiya.


Daga Abbas Adamu


SOURCE /CREDIT /Rariya on Facebook search. 

0 Response to "Duk Wanda Bai Ji Dadin Hukuncin Da Aka Yi Wa Abduljabbar Ba, To Lallai Ya Tuntubi Imaninsa, Cewar Shèik Sani Rijiyar Lemo"

Post a Comment