--
Ba Gudu Ba Ja Da Baya Kan Dokar Ƙayyade Cirar Kuɗi Saboda Shugaba Buhari Na Farin Ciki Sosai Da Ita, Cewar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Emefele

Ba Gudu Ba Ja Da Baya Kan Dokar Ƙayyade Cirar Kuɗi Saboda Shugaba Buhari Na Farin Ciki Sosai Da Ita, Cewar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Emefele

>

Ba Gudu Ba Ja Da Baya Kan Dokar Ƙayyade Cirar Kuɗi Saboda Shugaba Buhari Na Farin Ciki Sosai Da Ita, Cewar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Emefele

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Mista Godwin Emefele ya bayyana cewa babu gudu babu ja da baya dangane da dokar da bankin ya ke son sanya wa na kayyade cirar kuɗi a Najeriya.

Mista Godwin Emefele ya bayyana haka a Daura a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a garin Daura, jihar Katsina yau Alhamis a ziyarar da ya kaiwa shugaba Buhari a Mahaifarsa.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya,(CBN) ya kara da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na matukar jin dadi sosai kan wannan sabuwar doka ta takaita yawon da tsabar kuɗi ke yi, don haka za mu cigaba da gudanar da aikinmu ba tare da jin tsoro ba ko shakkun mutum ko wani gungun mutane ba, saboda muna da goyan bayan shugaba Buhari. 

Me zaku ce?

Credit /Jaridar. Mikiya Hausa via Facebook. 

0 Response to "Ba Gudu Ba Ja Da Baya Kan Dokar Ƙayyade Cirar Kuɗi Saboda Shugaba Buhari Na Farin Ciki Sosai Da Ita, Cewar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Emefele"

Post a Comment