--
Yadda za'a hada sabulun gyaran Jiki mai kyau a gida:

Yadda za'a hada sabulun gyaran Jiki mai kyau a gida:

>


Image source /credit /Facebook 
 HADIN SABULUN CIKIN SAUKI:


 


Yadda za'a hada sabulun gyaran Jiki mai kyau a gida:


Yana da kyau mata su san yadda ake hada irin wannan sabulun domin gyaran jiki ko kuma don sana’a.


 Yawan shafe –shafe yana bata fatar jiki don haka idan ana shafa abu kadan a fatar jiki, ya fi amfani da kuma gyaran fata. A yau mun kawo muku hanyoyi daban-daban wadanda za a yi amfani da sabulun salo don gyaran fata.


Abubuwan da za a bukata:


•Sabulun salo


•Zuma


•Bitamin E


•Man almond (za a iya samun sa a shagunan kayan kwalliya)


Hadi:


A daka sabulun salon ko kuma a saka abin kankare kubewa a kankare. Sannan a zuba ruwa domin ya narkar da sabulun. Sannan a zuba ‘bitamin E’ da man ‘almond’sai a kwab su sosai. Irin wannan hadin na gyara fatar jiki da kuma sanya ta subul da laushi.


Hadi na 2


•Sabulun salo


•Man kadanya


•Ruwan ganyen ‘aloe bera’


A narka man kadanya a ruwan zafi sannan a narkar da sabulun salon shi ma. A samu gora a zuba hadin man kadanyar tare da na man kadanya da ruwan ganyen ‘aloe bera’ sannan a girgiza su domin su hadu sosai.


Za a iya amfani da shi nan take daga gama hadi ko kuma a zuba a bar shi tsawon sati biyu sannan a fara amfani da shi.


Hadi na 3:


•Sabulun salo


•Zuma


•Kurkum


•Man kwakwa


•Man Zaitun


Bayan an narkar da sabulun salo a ruwan zafi, sai a zuba zuma da kurkum da man kwakwa da kuma man zaitun. A zuba su a cikin gora sannan a girgiza sosai domin su hadu sosai,sannan sai a zuba a murta.


Za a iya amfani da wannan hadin nan take ko kuma a jira ya yi tauri bayan sati biyu sannan a fara amfani da shi.


Wannan hadin yana magance kurajen gumi ko na fuska da wasu cututtukan fata.


Yadda za'a magance matsalan tabo a Jiki Akwai hanyoyi da dama wanda za a bi don magance tabo a fata amma a yau na kawo muku hanyoyi masu sauki domin magance tabo a fata. Idan tabo ya yi yawa a fatar mace, yana boye kyawunta ,don haka ya kamata a kula da fatar jiki sosai. Ga abubuwa biyar da za a yi amfani da su domin magance tabo a fata kamar haka:


 •Kurkum: A sami kurkum sai a hada shi da madarar ruwa yadda zai yi kauri sannan a shafa a kan tabo.


 A bar shi kamar tsawon minti biyar zuwa goma sannan a wanke. 


A ci gaba da shafa wannan hadin sau biyu a rana kamar tsawon watanni uku ko hudu. 


•Lemon tsami: A yanka lemon tsami gida biyu sannan a yaryada masa siga sannan a dirza shi a kan tabon na tsawon minti biyar. 


•Ganyen ‘Aloe bera’: A matse ruwan da ke cikin ganyen ‘aloe bera’ sannan a shafa a tabo na tsawon lokutan da za a iya bari, sannan sai a wanke. 


A rika yin hakan kamar sau biyu ko uku a rana . Sannan za a iya ci gaba da yin hakan har tsawon watanni uku. Source /credit /Sirrin rike miji on Facebook. 0 Response to "Yadda za'a hada sabulun gyaran Jiki mai kyau a gida:"

Post a Comment