--
Wani Dan Kasuwa A Kano Ya Bada Gudummawar Motocin Daukar Gawa Guda Uku

Wani Dan Kasuwa A Kano Ya Bada Gudummawar Motocin Daukar Gawa Guda Uku

>

 Wani Dan Kasuwa A Kano Ya Bada Gudummawar Motocin Daukar Gawa Guda Uku


Wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Jamilu Kabiru ya saya wa al’ummar Karamar Hukumar Bichi dake Jihar Kano motocin ɗaukar gawa guda uku da babura guda biyar.


Kabiru, wanda a ka fi sani da Sabon-shafi, ya bada ababen hawan ne ga wasu kauyuka da su ke wahalar samun motar kai gawa a Bichi.


Da ya ke jawabi a wajen miƙa mukullayen motocin ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, Sabon-shafi ya ce ya bada sadakar motocin ne sabo da wata rana ya ga an dauko gawa a kan babur mai ƙafa uku.


A cewar sa, yana tafiya sai ya ga an dauko gawar a babur mai ƙafa uku har kafafun mamacin na fito wa waje a kan hanyar su ta zuwa binne gawar.


“Wannan dalili ne ya sa na ci alwashin sai na kawo karshen karancin motar kai gawa a wasu sassa na Bichi,” in ji shi.

Ya ce baburan kuma guda 5 ya bada su ne kyauta ga ma’aikatan makabarta domin su rage wahalar zuwa wajen aikin nasu na hakar kabari.


A jawabin Hakimin Bichi, Alhaji Abdulhamid Bayero, yayin gabatar da Alhaji Jamilu Sabon-shafi a gaban sarki, a madadin Sarkin, ya yaba masa a bisa wannan kokari da yayi tare da yi masa addu’ar fatan alkairi.


Daga Daily Nigerian

SOURCE 👇

Rariya on Facebook. 

0 Response to "Wani Dan Kasuwa A Kano Ya Bada Gudummawar Motocin Daukar Gawa Guda Uku"

Post a Comment