--
 Wadi-us-Salam, maƙabarta mafi girma a Duniya a Ƙasar Iraqi.

Wadi-us-Salam, maƙabarta mafi girma a Duniya a Ƙasar Iraqi.

>

 


Wadi-us-Salam, maƙabarta mafi girma a Duniya a Ƙasar Iraqi.


Daga Mahmud Habibullah Taskar Nasaba.


Wadi-al-Salaam ( Larabci: وادي السلام,) Wādī al-Salām, maƙabarta ce ta Musulunci, da ke cikin birnin Najaf na ƴan mabiya Shi’a mai tsarki a ƙasar Iraq, ita ce maƙabarta ma fi girma a duniya.


Maƙabartar ta na da kadada (1,485.5 (601.16 ha; 6.01 km 2 ; 2.32 sq mi), kuma ta ƙunshi gawarwaki sama da Miliyan Biyar. Haka nan, ta na jan hankalin miliyoyin musu a shekara.


Maƙabartar ta na kusa da hubbare Sayyidina Ali ibn Abi Talib ( RTA) Imam Halifa na huɗu. Don haka, da yawa daga cikin ƴan Shi’a a Iraq sukan nemi a binne su a wannan maƙabarta. Sakamakon ingantattun hanyoyin sufuri, ana binne ƴan Shi’a daga sassa daban-daban na duniya (ko neman a binne su) a maƙabartar.


An shafe shekaru sama da Dubu Ɗaya da Ɗari Huɗu (1,400yrs) ana jana’izar yau da kullum, kuma wurin ya na cikin jerin abubuwan tarihi na Cibiyar Kula Da Adana Kayan Tarihi na Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO).


An yi ƙiyasin cewa, a lokacin yaƙin Iraƙi ana binne gawarwaki kimanin Ɗari Biyu, zuwa Ɗari Biyu da Hamsin, a kowace rana, duk da haka, a cikin shekarar Dubu Biyu da Goma (2010) wannan adadin ya ragu zuwa ƙasa da mutum Ɗari.


Kimanin sabbin gawawwaki Dubu Hamsin (50,000) ne ake shiga cikin maƙabartar kowace shekara daga ko’ina cikin duniya.


Wannan adadi ya haɓaka a kan kusan gawarwakin Dubu Ashirin (20,000), musamman daga Iran, waɗanda a da ake haɗa su kowace shekara a farkon ƙarni na Ashirin.


Mafi akasarin ƴan Shi’ar Iraƙi da Iraniyawa da yawa su na da wani dangi da aka binne a maƙabartar aƙalla.

SOURCE 👉 ALFIJIR HAUSA ON FACEBOOK. 


0 Response to " Wadi-us-Salam, maƙabarta mafi girma a Duniya a Ƙasar Iraqi."

Post a Comment