--
MALAMAN JAMI’A NA SHIRIN KOMAWA YAJIN AIKIN SAI BABA TAGANI

MALAMAN JAMI’A NA SHIRIN KOMAWA YAJIN AIKIN SAI BABA TAGANI

>




IMAGE SOURCE :RAHAMA TV ON FACEBOOK 

Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU na shirin sake komawa yajin aiki bayan da ta zargi gwamnati da rashin cika alkawarinta na biya musu bukatunsu.

A wata tattaunawarsa da 'Yan jaridu mataimakin shugaban kungiyar ASUU, Dr Chris Piwuna, ya ce kungiyar na shirin gudanar da taron gaggawa domin yanke shawara a kan matakin da za ta dauka a cikin kwanakin nan.


Malaman na korafi kan yadda suka ce gwamnati ba ta biya su albashin wata takwas da suka yi suna yajin aiki ba.


ASUU ta ce babu ko daya daga cikin alkawuran da suka yi da gwmnati ta cika.


Shin ku na ganin ya dace Gwamnati  ta ba Malaman rabin Albashi na watan Oktoba?


Shin wanne mataki ASUU ya kamata ta dauka akan hakan?


SOURCE :RAHAMA TV ON FACEBOOK 

0 Response to "MALAMAN JAMI’A NA SHIRIN KOMAWA YAJIN AIKIN SAI BABA TAGANI"

Post a Comment