--
 illolin amfani da macen daba takaba, neman matan banza ( zina)

illolin amfani da macen daba takaba, neman matan banza ( zina)

>

ILLOLIN ANFANI DA MACE WACCE BA MATARKA BA KO YIN NEMAN MATA A TAKAICE.


A kimiyance bayan sanin Zina tana cikin manyan zunubai ko laifukan da Allah yai Hani da mugujesu. A bangaren kimiyya ma akwai ababen da mazaje masu wannan dabi'ar ke korafi ko fassara kansu da sunan basuda cikakkar lafiya.


- Saurin inzali:- Anxiety wato fargaba Yana Daya daga cikin abunda ke haifar da wannan Wanda Yana daga aikin kwakwalwar mutum ne, Tinanin kada a kama mutum, ko kada wani yazo ya samesu da Rashin kwanciyar hankali lokacin da ake barnar Yana kan gaba wajen haifar da saurin inzali Dan Haka wadanda suka fahimci wannan basuda matsala idan sukai aure zai daina Amma su sani barna suke aikatawa.


-Yaduwar Cutuka:- hanyace mafi sauki wacce ake yayar dinbin Cutuka daga wani zuwa wani daga ciki akwai Wadanda idan aka hadu dasu tofa maganin su saidai Allah, Dik lokacin da jaraba ta samemu murika Tina wannan matsalar na dinbin cutukan da zamu iya dauka cikin kankanin lokaci mu dauki lokaci Mai tsawo muna wahala ko har iya rai ma.


- Shigar Ciki:- A bangaren Mata Babu abu mafi Muni ga mace ta fara daukan cikin shege Kuma yazama dabi'ar ta shine ta samu ta zubar alhali batayi auren sunna ba, a rayuwa Bata fara da cikin sunna ba akwai tabewa Allah ya kiyashemu. Zubar da ciki ga Mata abune Mai hatsari ga rayuwar su Mata kusani yawan zubar da ciki zaikai ga rasa Rai.


- Yin Asarar Kudi:- Cikin minti 5 kun gama Amma daga karshe wannan zai iya sa kayi ta asara da kashe kudi ga abokiyar aikin ka, duk lokacin da way bukata ta taso Kai zakayi dole saboda tsoron kada ta Tona maka asiri, shiyasa maza masu neman Mata Basu arziki idan kuwa sunyi to rabonsu ne suke cinyewa kajira kaga karshesu. Ya Allah kayi Mana tsari ka Kara karemu, ya Allah ka shiryar damu hanya madaidaiciya.

Da fatan Zamuyi Juma'a lafiya


(Kabir Yusuf Danwurin Dutsi)

Source 👉sirrin rike miji on Facebook. 

0 Response to " illolin amfani da macen daba takaba, neman matan banza ( zina) "

Post a Comment