--
Ga Dalilan dasuke sa saurin kawowa wato release ga mazaje

Ga Dalilan dasuke sa saurin kawowa wato release ga mazaje

>





Image source /credit Facebook. 

FARGABA, RASHIN NATSUWA DA GAGGAWA Na daga cikin ababen Dake Haifar da Saurin Kawowa wato Release ga Mazaje.


An fassara matsala ta rashin haihuwa ga iyalai a Matsayin Wadanda sukai aure suka kwashe watanni 12 suna tare, suna Mu'amula ta aure ba tareda Samu ko alamum ciki ba. Daga wannan Lokacin za a fara sa alamar Tambaya, za a fara zargi ko tinanin Ina matsala take.


A al'adar mu ta Hausa Fulani in Banda yanzu da zamani yazo ma'aurata zasu iya kwashe Shekara cur Basu gama sanin juna ba, saboda tsabagen kunya da Kuma Karancin shekaru, a da akanyi ma diya aure da wuri, akwai tsantsar kunya tsakanin iyalai sai kaga ko sunan miji mace Bata iya fadi saboda kunya balle watanni da aure Kaji mace ko miji na Maganar ko batan wata, ni ban samu ciki ba zamani kenan.


Matar da Dake danya Shar duk yanda da namiji yake da kokari ko yasan Mu'amula ta aure bazai iya kaiwa gareta ba cikin kankanen lokaci saboda rashin sabo. Akwai dinbin ababen Dake sa mace budewa tin tana gida duk da Bata taba Sanin Wani da Namiji a Duniya ba. 


Dan haka Ma'aurata Abi Sannu, Mazaje acire Fargaba, Kagara, ko GAGGAWA ga iyalai, Kwakwalwa ta dauka matar kace, ibada Ake sannan Kuna tare har abada, Abunda Ake zumudin shi ba abinci bane da zai kare ko ace yau kayi Anfani dashi gobe sai ka siyo Wani. 


An halatta mana iyalanmu da daddare, da safe, da Yamma ko Dara, cikin sanyi ko da zafi. Dan haka kasa da wata 12 da aure Bai Kamata a fara zargin matsala ta rashin haihuwa ba. 


Da fatan wadanda sukai wannan tanbayar sun fahimta.

✍️

Daliba Mai hazaka 

Via Ustaz Usman


Source /credit/sirrin rike miji on Facebook. 

0 Response to "Ga Dalilan dasuke sa saurin kawowa wato release ga mazaje "

Post a Comment