--
Dalilin da ya sa 'yan Arewa ba sa samun bashin bankin raya ƙasa a Najeriya

Dalilin da ya sa 'yan Arewa ba sa samun bashin bankin raya ƙasa a Najeriya

>

 

Kwamitin Majalisar Dattawa ta Najeriya da ke kula da harkokin bankuna ya yi ƙarin bayani kan dalilin da ya sa yankin arewacin Najeriya ba ya samun rancen da bankin raya ƙasa yake bayarwa kamar yadda yankin kudu ke samu.


A makon da ya wuce ne Majalisar ta kafa wani kwamiti domin ya gudanar da bincike kan zargin cewa bankin ya mayar da arewa saniyar-ware.


Sanata Ali Ndume ne ya gabatar da ƙorafin yayin zaman Majalisar, yana mai cewa daga cikin kusan naira biliyan biyar da bankin ya raba, kashi 11 cikin 100 kacal ya bai wa jihohin Arewa.


Sai dai a tattaunawarsa da wakilin BBC Ibrahim Isa, shugaban kwamitin Sanata Uba Sani ya ce rashin bankuna mallakin yankin da ƙyamar kuɗin ruwa saboda dalili na addini na cikin abubuwan da suka sa yankin Arewa ba ya cin gajiyar rancen sosai.

SOURCE 👇

BBC Hausa on Facebook. 

0 Response to "Dalilin da ya sa 'yan Arewa ba sa samun bashin bankin raya ƙasa a Najeriya"

Post a Comment