--
AYYUKAN GWAMNA MAI MALA: Gani Da Ido Ya Kori Ji (Kashi Na Uku)

AYYUKAN GWAMNA MAI MALA: Gani Da Ido Ya Kori Ji (Kashi Na Uku)

>







Daga Comrd Hassan Peppe Yobe 


A cigaba da kawo muku aikin alheri na mai girma gwomnan Jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni,CON. (Chiroman Gujba ). Ya gwangwaje al'umman Gulani da sabuwar asibiti (General Hospital) wanda shi ne na farko a tarihin karamar hukumar gulani dake jihar yobe.




Gwamnati Buni a yanzu haka ya kammala aikin asibitin gaba daya sannan da sanya kayan aiki na zamani masu inganchi wanda ake bukata a cikin asibitin.


Wannan asibitin ya zama abun alfahari da jin dadi a gurin al'umman Gulani baki daya, sabida  abaya can idan akwai marar lafiya mai tsanani ko mace mai juna biyu wanda sai an ma ta aiki ko wani abu makamanci haka to dole sai an kawo ta/shi zuwa garin Buni Yadi ko Damaturu kafin a samu abunda ake bukata.




Lallai gwamna buni yacikawa al'ummar gulani burinsu sakamakon irin abubuwan alkhairai da cigaba yasamar a Karamar hukumar, yakai musu wutan lantarki, ruwan sha, taimakawa matasansu, babban masallacin jumma'a, dadai sauransu, Gwamna Mai Mala Buni Sarkin Aiki,




Kudos to workholic Governor Honorable Mai Mala Buni is working Yobe is Moving forward.

0 Response to "AYYUKAN GWAMNA MAI MALA: Gani Da Ido Ya Kori Ji (Kashi Na Uku)"

Post a Comment