--
Martani Kan Kisar Harira Da Yaranta 4 Da 'Yan Ta'adda Suka Yi a Anambra:-Cikakken Bayani

Martani Kan Kisar Harira Da Yaranta 4 Da 'Yan Ta'adda Suka Yi a Anambra:-Cikakken Bayani

>


 Alhaji Sa’ad Abubakar III, Sarkin musulmi ya koka akan kisan Harira Jibrin, da yaranta hudu a Isulo cikin karamar hukumar Orumba ta Arewa da ke cikin Jihar Anambra da wasu ‘yan bindiga su ka yi.


Sultan wanda ke shugabantar Jama’atul Nasril Islam, JNI ya yi suka kwarai akan kisan inda ya ce rashin hankali da kauyanci ne, The Punch ta ruwaito.


Ya roki Gwamnatin Tarayya akan ta dage wurin ganin ta gano ‘yan bindigan da su ka yi aika-aikan a maboyarsu cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.


Sultan din shugaba ne ga duk Musulman Najeriya kuma ya bayyana alhininsa kwarai akan kisan rashin imanin da ake ta yi a kasar nan saboda rashin tsaro.


The Punch ta ruwaito yadda wani bangare na takardar da JNI ta saki ya zo kamar haka:


“A maimakon Shugaban kungiyar, Mai girma Sultan na Sokoto, Alhaji(Dr.) Muhammad Sa’adu Abubakar, CFR, mni, Jama’atul Nasril Islam ta yi alawadai da rashin hankali, kauyanci da kuma mummunan kisan da aka yi wa wata Harira Jibrin; mace mai ciki da yaranta guda hudu a Isulo da ke karamar hukumar Orumba ta Arewa da ke Jihar Anambra.”


A cewarsa:


“Lamarin kari ne akan kashe-kashen da ake ta yi wa mutane da dama, musamman musulman jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya.


Abin alawadai ne yadda ake ta nuna rashin imani ta hanyar halaka rayuka a kasar nan. “Cikin radadi, JNI ta kula da yadda musulman kirki 'yan kasuwa har da dabbobinsu su ke fama a yankin.


 Wannan alama ce ta tsana da rashin imanin da ake nuna musu. JNI ta na ganin lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta yi kokarin daukar mataki.”


Ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta zage damtse wurin hukunta duk wadanda ke da hannu a kashe-kashen Kudu maso Gabas kafin lokaci ya kure. Ya ci gaba da cewa wajibi ne a gwamnati ta dauki mataki ta hanyar ratsa dazuka da maboyun ‘yan ta’addan don gano su. Kuma hakan ne zai sanya a tauna tsakkuwa don aya ta ji tsoro.

0 Response to "Martani Kan Kisar Harira Da Yaranta 4 Da 'Yan Ta'adda Suka Yi a Anambra:-Cikakken Bayani "

Post a Comment