--
Daga karshe dai Sheikh Nuru Khalid Yajefa Qalu-bale akan masu sanya baki Kan Ganin Wata--

Daga karshe dai Sheikh Nuru Khalid Yajefa Qalu-bale akan masu sanya baki Kan Ganin Wata--

>


 Me Yasa Sheikh Dahiru Bauchi Kowace Shekara Sai Ya Kawo Rudani A Cikin Al'ummar Musulami ?


A cikin shekarun nan duk sanda sarkin musulmai ya bayyana rashin ganin watan shawwal, shi Sheikh Dahiru Bauchi sai ya kawo sabanin haka, alhali sarkin musulmai yana matukar girmama shi.



Koda sanarwan da mai martaba ya fitar na duban watan Ramadan, akwai lambobin manyan malamai da aka aminta dasu da zarar anga wata a sanar musu, su kuma su aikawa sarkin musulmi ya sanar, lambar Sheikh Usman Dahiru Bauchi, tana cikin takardar, wanda hakan yana nuna cewa, babu shakka sarki yasan da matsayin sa.


To amma meyasa shi shehu baya ganin haka ya girmama lafuzan sarki da umarnin sarki, tare da yi masa biyayya a matsayin sa na sarkin musulman Nigeria?


A cikin audio da mukaji munji shehu yana umarnin a turawa sarki sako, wato dalibansa sun nado muryar shi sun watsa tun kafin fadar sarki ta samu labari.



Kuma abun haushi sunki sakin audio da zai kawo rudani a cikin al'ummar musulmai sanda sarkin musulmai, Sa'ad Abubakar lll ya sako jawabi akan ba'a ga wata ba.


Meyasa shehu yana haka? Allah kadai ya sani.


Duk da cewa, wasu na ganin cewa, "Hakan baya nasaba da, maganganun shehu a baya yana zargin sarki da karkata i zuwa ga izala, inda har ya taba kiran sarkin Musulmai da sarkin izala.


Duk da cewa, a zahirin al'amari ba haka ba, sarkin musulmai yana kokarin adalci a dukkanin akidu ma banbanta.


Amma tun daga kalaman shehu, har zuwa yanzu kowace shekara sai shehu Dahiru Bauchi, ya sabawa mai girma sarkin musulmai.


Dan haka hakkin ganin wata yana hannun sarkin musulmai, da kwamitin da aka tsara, kuma masana abun. Amma shi shehu baisan komai akan wannan sha'ani ba, nidai a ganina na kusada shehu suna son hura rikici a tsakanin sa da mai martaba sarki ne, yo in ba hakaba, meyasa basuyi maza su turawa sarki?


Duk wanda yabi Sheikh Dahiru Bauchi wajen aje azumi yayi kuskure,  kuma ya sabawa Allah wajen fadinsa ayi da'a ga shuwagabanni,  kuma sarkin musulmi shugaba ne, shehu kuma akasin haka.

0 Response to "Daga karshe dai Sheikh Nuru Khalid Yajefa Qalu-bale akan masu sanya baki Kan Ganin Wata--"

Post a Comment