--
Babbar magana: Kotu ta umurci bankin Polaris daya biya wata kwastoma diyyan N500,000 sakamakon bata mata lokaci da suka yi wurin mayar mata da kudaden ta da suka makyale

Babbar magana: Kotu ta umurci bankin Polaris daya biya wata kwastoma diyyan N500,000 sakamakon bata mata lokaci da suka yi wurin mayar mata da kudaden ta da suka makyale

>


Kotu ta umurci bankin Polaris da ta biya wata kwastoma diyyan N500,000 sakamakon bata mata lokaci da suka yi wurin mayar mata da kudaden ta

Wata babbar kotu a jihar Akwa Ibom ta umurci bankin Polaris da ya biya wata kwastoma Naira 500,000 a matsayin kudin diyya sakamakon gazawar su wajen amfani da (POS) tun da ya wuce sa’o’i 72 kamar yadda doka ta tanada.

Mai karar Idongesit Nwoko, ta kasance ma’aikaciyar gwamnati ce a garin Akwa Ibom inda take amfani da bankin polaris a mastayin wurin ajiyanta.


Ta yi karar Bankin a kotu


Ta ciro Kudi Naira 61,000 ta hanyar amfani da POS a ranar 24 ga watan Disamba, 2020,Banki sun cire kudi amma kudi bai iso hannun ta ba.

Misis Nwoko ta yi ta fafutukar ganin ta samu kudinta inda ta ziyarci bankin lokuta da dama,sai bayan kwanaki 28 sannan Bankin suka dawo mata da kudaden ta.

Iri yadda Bankin su ka bata mata lokaci yasa, matar ta hannun lauyanta, Utibe Nwoko, ta maka Bankin a Kotu.


Ta nemi a biyata Diyya


Misis Nwoko ta roki kotun da ta tilasta wa bankin su mayar mata da kudin ta.

Ta kuma bukaci kotun da ta tilasta wa bankin ya biya ta Naira miliyan 100 a matsayin diyya da kuma Naira miliyan 1 a matsayin kudin bata mata lokaci da sukayi.

Mai shari’a Bennett Ilaumo, a hukuncin da ta yanke, ta umurci bankin da ta biya N500,000 a matsayin diyya ga Misis Nwoko saboda gazawar Bankin wajen warware ciniki matsalar cikin sa’o’i 72 kamar yadda doka ta tanada.


Martanin lauyan wanda ake tuhuma


Anthony Ebuk, lauyan wanda ake tuhuma, ya shaida wa PREMIUM TIMES, cewar wanda yake karewa wato Bankin polaris za su daukaka kara kan hukuncin.


Kudin ta Bai kai abinda za a ce mu biya diyya ba


Mai magana da yawun bankin Polaris, Rasheed Bolarinwa, ya bayyana Cewa asarar N500,000 rashin daidai to ne idan aka kwatanta da N61,000 da aka rike mata.

Ya ce bankin ya na nazarin akan hukuncin kuma zai dauki “matakan da suka dace na doka”.

0 Response to "Babbar magana: Kotu ta umurci bankin Polaris daya biya wata kwastoma diyyan N500,000 sakamakon bata mata lokaci da suka yi wurin mayar mata da kudaden ta da suka makyale"

Post a Comment