--
 A Bauchi, wani mutum ya yi garkuwa da diyar makwabcinsa kuma ya kasheta bayan karban kudin fansa

A Bauchi, wani mutum ya yi garkuwa da diyar makwabcinsa kuma ya kasheta bayan karban kudin fansa

>


 

A Bauchi, wani mutum ya yi garkuwa da diyar makwabcinsa kuma ya kasheta bayan karban kudin fansa


Irin abinda ya faru a Kano, wani mutumi ya sace diyar makwabcinsa a Bauchi kuma ya karbi kudin fansa Yawale ya bukaci kudin fansa amma bayan karba ya kashe yarinyar kuma ya birneta cikin gidansa Jami'an hukumar tsaro sun damkeshi tare da abokinsa kuma zasu gurfana gaban kuliya


Toro, Bauchi - Jami'an tsaro sun damke wani mutumi mai suna Kabiru Abdullahi wanda ake zargi da kisan diyar makwabcinsa, Khadija yar shekara biyar a jihar Bauchi.


Kakakin hukumar Civil Defence na jihar, Garkuwa Adamu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Litinin, rahoton ChannelsTV. 


Ya yi bayanin cewa an damke Abdullahi ne tare da Alhaji Yawale kan zargin garkuwa da diyar Abdullahi Yusuf a Sabon Gari Narabi a karamar hukumar Toro.


Adamu yace: "Bincike da aka fara sun nuna cewa Kabiru Abdullahi ya sace Khadika a gaban gidansu kuma ya shaketa ya jefata cikin buhu."


"Sai ya tuntubi mahaifinta Abdullahi Yusuf ya bukaci kudin fansa. Bayan tattaunawa, sun amince kan N150,000 don a saketa."


A cewar Kakakin NSCDC, Yawale ya karbi N150,000 karkashin bishiyar tsamiya a garin Narabi. Yace: "Bincike ya kara nuna mana cewa an kashe Khadija ranar 27 ga Afrilu, 2022, kuma ya birneta dakin girkin abinci a gidansa." "Masu bincike sun hako gawarta kuma sun kai asibitin Toro."

0 Response to " A Bauchi, wani mutum ya yi garkuwa da diyar makwabcinsa kuma ya kasheta bayan karban kudin fansa"

Post a Comment