--
Ku Isar Ma Mahassada Da Masu Son Zuciya Gamida Masu Ƙaramin Fahimta Gameda Shari'ar Musulunci!

Ku Isar Ma Mahassada Da Masu Son Zuciya Gamida Masu Ƙaramin Fahimta Gameda Shari'ar Musulunci!

>


 Ku Isar Ma Mahassada Da Masu Son Zuciya Gamida Masu Ƙaramin Fahimta Gameda Shari'ar Musulunci!

______________________________________


✍ Ibrahim Shehu Giwa. 


Duk da Lokaci yamin karanci A yanzu, hakan ya sa ban son tanka abubuwa da dama, amma yana da kyau inyi tsokaci akan wanda sukai ta cece-kuce kan Tafseer na maata da Mal. Zainab Sheikh Ja'afar Adam (Rahimahullah) ta fara.


1. Ina suka manta manyan mata da suka koyar da ilimi, Nana Aisha R.A ta ruwaito hadisai 2,210 ita kadai, kuma ta karantar har tsawan rayuwar ta, haka sauran manyan sahabbai mata.



2. Imam Malik da sauran manyan malaman musulunci sun yi karatu wajen mata kaman shi ya koyi hadisi daga Fatima Bnt Saad Almadaniyyah, Imam Muhammad Bn Shihab al-Zuhri ya yi karatu wajen Amrah bnt Abdulrahman, Imam al-Dhabi da  Ibn Qayyim al-Jawziyyah daga Fatima Bnt Jauhar da sauran  magabata na kwarai. 

(Ka duba Tahzeeb al Tahzeeb 

na Ibn Hajar, Tazkirah al Huffaz na Imam al-Dhahabi da Ibn Qayyim Al-Jawziyyah: Hayatuhu Atharuhu Wa Mawariduhu na Bakr Abu Zaid).


3. A nan kasar Hausa, Nana Asma'u diyar Sheikh Uthman bn Fodio tana daga cikin manyan malamai da suka karantar a zamanin ta, matar Sheikh Abdulwahab Abdallah, Sheikh Aminu Daurawa da sauran su duk sun karantar a wannan kasar.


4. Masu wannan korafi fa are comfortable mata na aikin jarida, wasun su na siyasa, wasu na kasuwanci, wasu na aikin gwamnati wasu ma na lecturing a jami'a ko aikin asibiti, amma damuwan su me ze sanya mace ta koyar da addini ma mata yanuwanta, dukda ga manyan matan sahabbai da magabata sun koyar da ba ma mata ba harda maza.

5. Wato matsalar don diyar Sheikh Jafar ce shine ake cece kuce, dukda tayi shiga na kamala, babu cakudedeniya na maza da mata, wanda yin suka ga abu don wane ke yi na da mummunar illa.


6. A karshe, addinin musulunci ba bagidajen addini bane, ya baiwa mata damarmaki da dama, na su koyi ilimi  su karantar (Nana Aisha), suyi kasuwanci (Nana Khadija) suyi tambaya (Surah Mujadala), har jihadi sunyi (Ummu Ammarah -Nusaybah), suyi addini, su mallaki kaddarori da gidaje, suyi harkokin rayuwa matukar zasu kiyaye mutuncin su.


7. Karanta hakikanin tarihin manzon Allah da kyakkyawan fahimtar addini, da karanta tarihin mata da sahabbai mata na manzon Allah, da magabata na kwarai ze ba da kyakkyawan fahimtan yanda addinin musulunci ya baiwa mata damammaki, kuma ya daga darajar su sama da kowane addini ko civilization a duniya.


8. Allah ya bamu ilimi me anfani, ya kuma anfanar da mu abinda Malama Zainab da sauran malamai zasu koyar da mu a wannan wata me albarka da sauran watanni.


Naku:


Ibrahim Shehu Giwa.

11th Ramadan 1443AH

12th April 2022.

0 Response to "Ku Isar Ma Mahassada Da Masu Son Zuciya Gamida Masu Ƙaramin Fahimta Gameda Shari'ar Musulunci!"

Post a Comment