--
Da Dumi-Dumi:- Watan Ramadan zai cika kwana 30 a Nigeria da kasar Saudi Arabia

Da Dumi-Dumi:- Watan Ramadan zai cika kwana 30 a Nigeria da kasar Saudi Arabia

>

 

Daga Adamu Ya'u Dan America


Idan baku manta tun shekaran da ya wuce lokacin da muka kammala Azumi 30 na sanar da ku cewa idan Allah ya kawo mu Wannan shekara, shi ma akwai wani Dama na sake samun Azumi 30 idan har an dauki Azumi a ranar Asabar (02/04/2022).


Dukkan mu Nigeria da Saudiyya idan Allah ya kaimu ranar 29 ga Watan Ramadan, Wata zai riga Rana Faduwa.


Na Tabbata Saudi_Arabia Ba za su ga Wata a ranar Duban Fari ba, kuma babu wanda zai yi musu Tawaye.



Amma mu a Nigeria kusan Abinda ya faru a wanchan shekarar ina tunanin zai sake faruwa, kamar yadda wanchan shekarar muka tabbatar Babu Wata a Sama Bayan Faduwar Rana a ranar Duban Fari, amma a haka aka samu wasu wai Sun ga Wata.


Kuma wasu da basu san meye ilimi akan wata ba suna ta sukar Mai Alfarma Sarkin Musulmi akan wai anga wata yaki tabbatar wa, Daman ai ba zai amince ba, saboda yanzu ilimi yazo ba yadda za'a yi amfani da cewa anga wata Alhali babu wata a ranar.


Ga bayanin Tsayuwar jinjirin Watan SHAWWAL din.


Idan Allah ya kaimu ranar Asabar Mai zuwa (29 ga Watan Ramadan 1443AH) daidai da (30/04/2022) #Duniyar_Wata zai yi #Crossing_Conjunction tsakanin #Duniyar mu da #Rana, da misalin karfe 9:28pm na Dare.



Sannan a wannan lokacin babu haske ko kadan a jikin Watan, wato yana (0.0%)ne.


Kafin wannan Conjunction din a ranar Asabar din a nan Jimeta-Yola Nigeria Watan zai Fadi misalin karfe 6:11pm na yamma,


Rana kuma zai Fadi karfe 6:21pm na yamma,


A Kano Watan zai Fadi karfe 6:30pm, Rana kuma zai Fadi karfe 6:39.


A Abuja Watan zai Fadi karfe 6:31pm, Rana kuma zai Fadi karfe 6:40pm


A Port Harcout Watan zai Fadi karfe 6:29pm, Rana kuma zai Fadi karfe 6:37pm


A Sokoto Watan zai Fadi karfe 6:44pm, Rana kuma zai Fadi karfe 6:53pm


A Lagos Watan zai Fadi karfe 6:46pm, Rana kuma zai Fadi 6:54pm


Kun ga kenan Watan zai riga Rana Faduwa da mintuna 10, a wasu jihohin mintuna 9, wasu kuma mintuna 8 Lokacin ma watan bai zama Jinjirin wata ba yana #Black_Moon, ma'ana Babu Wata a sama Bayan Faduwar Rana.


Wannan Dalilin shi yasa ba yadda za a yi mutun yace ya ga Wata a yadda, saboda babu ma Watan a sama bayan Faduwar Rana.


Haka a kasar Saudi Arabia wanda suma ranar Asabar din ne 29 ga Watan Ramadan, Duk da Telescope din su a ranar Asabar din Watan ba zai Ganu ba, saboda suma a wajen su Watan zai riga rana Faduwa da mintuna 15, Wata zai Fadi karfe 6:30pm Rana kuma zai Fadi karfe 6:45pm a #Makkah da Sauran Jihohin Kasar duka, kun ga kenan bayan Faduwar Rana babu Wata a Sama,


Dolen su a ranar Asabar din za su sanar da cewa ba su ga Wata ba, hakan zai sa ranar Ranar Lahadi za su cika Azumi 30.


Amma a Washe gari Ranar Lahadi, Ranar da za a cika Azumi 30 wato daidai da (01/05/2022) bayan Faduwar #Rana anan Jimeta Yola Watan ya samu Awa 20 da minti 53 da yin Conjunction.


Rana Zai Fadi anan Jimeta karfe 6:21pm, Watan Kuma Zai Fadi Karfe 7:00pm, hakan na nuna cewa bayan Faduwar Rana Watan zai kai Mintuna 39 Kafin ya fadi,


Misalin Hakan ne a sauran Jihohin Nigeria bayan Faduwar Rana Watan zai kai mintuna daga 39 zuwa 42.


Hasken da zai bayyana a jikin Watan zai kasance (0.8%) hakan na nuna cewa za'a iya Ganin Watan da idon Dan Adam idan akwai yanayi mai kyau, a hakan ma sai daidaikum mutane ne za su iya gani saboda yayi matukar kankanta.


Hoto na farko ranar Asabar, ranar Duban Fari na Bayyana muku yadda za ku ga Watan yana Kasa da rana zai riga rana faduwa, babu Haske a jikin sa, shi yasa ba za a ga Watan a ranar ba.


Hoto na biyu ranar Lahadi Watan yana saman Rana, Hasken sa.


Hoto na uku ranar Litinin Wato ranar Sallah Hasken sa yana (3.4%) ya ninka na ranar Asabar sau 4, wanda hakan ne idan wasu mutane sun gani za su ce yanzu Wannan Watan ne za a ce jiya ya kama?


Saboda su a tunanin su tunda a ranar Lahadi Hasken sa yana (0.8%) suna so su ga cewa a ranar Litinin Hasken sa ya kasance (1.6%), ba su san cewa shi Wata ba haka yake kara Hasken sa ba, shi yasa ya kamata idan baka da ilimin abu bai kamata abinda tunanin ka ya baka kawai kace shi ne daidai ba, ya kamata mu nemi ilimin sanin abu kafin muyi magana akan abun.


Da fatan Allah ya sa mu Dace.

0 Response to "Da Dumi-Dumi:- Watan Ramadan zai cika kwana 30 a Nigeria da kasar Saudi Arabia "

Post a Comment