--
Zamu Kafa Majalissar Dinkin Duniya Ta Musulunci, Cewar Shugaban Turkiyya

Zamu Kafa Majalissar Dinkin Duniya Ta Musulunci, Cewar Shugaban Turkiyya

>


 



Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan, ya bayyana cewa tunda majalissar ɗinkin duniya, ba za ta iya share hawayen ƙasashen Musulmin duniya ba to bata da amfani suci gaba da zama a cikinta, duba da yadda ake ta hallaka musulmin ƙasar Palasɗinawa, wanda Isra'ila ke yi amma ba tare da majalissar ɗinkin duniya ta ɗauki wani mataki na hana faruwar hakan ba.


In ji Erdogan, ya zama wajibi mu kafa sabuwar majalissar ɗinkin duniya ta (Muslim United Nations? domin kuwa abubuwan da ake yi na kisan musulmi tare da aibata su da sunan ƴan ta'adda hakan ba abun da zamu kyale bane, in ji shi, a wani jawabi da yayi a daren jiya a kafar talabijin ɗin kasar.


Kunji fa shin kuna goyon bayan ɗaukar wannan  mataki kuwa?

0 Response to "Zamu Kafa Majalissar Dinkin Duniya Ta Musulunci, Cewar Shugaban Turkiyya"

Post a Comment