--
Yanzu-Yanzu:- Abdulmalik Tanko yasake Shiga cikin Bala'i, Yayiwa Jami'an tsaro karya.

Yanzu-Yanzu:- Abdulmalik Tanko yasake Shiga cikin Bala'i, Yayiwa Jami'an tsaro karya.

>


Ana wata ga wata:- Makashin Hanifa yana neman yiwa Jami'an tsaro Sharri

Malamin makarantar nan Abdulmalik Tanko da ake zargi da kashe dalibarsa Hanifa Abubakar ya ce, jami’an tsaro ne suka tursasashi ya amsa laifin da ake zarginsa.

Abdulmalik Tanko ya bayyana hakan a ranar Alhamis a gaban babbar kotun jiha Mai Lanba 5 dake sakatariyar Audu Bako Karkashin jagorancin mai Sharia mai Sharia Usman Na Abba.

A zaman kotun masu gabatar da kara sun ci gaba da gabatar da shaidu inda aka gabatar da jami’an tsaro daga sashin yaki da garkuwa da mutane kuma suka bada shaida.


Inda suka bayyana cewar sunyi musu tambayoyi batare da tursasamusu ba haka Kuma shima Abdulmalik Tanko ya bada bayaninsa inda ya bayyanawa kotu cewar shifa tilasata Masa akayi ya bada bayanansa a wancan lokaci.

Bayan kammala jin nasa bayanin itama Fatima Musa tace ganin abinda ya faru ga su Abdulmalik shi ne ya tsorata ta bada nata bayanin.

Daga karshe kotu taji bayanin kowane bangare bayanda Mai gabatar da Kara kwamishinan Sharia Barisata Musa Abdullahi Lawal yayi masa tambayar cewar duk bayanin daya fada a wajan bincike hakane? sai Yace haka ne.

Kotun ta dage ci gaba da zaman zuwa ranar 9 da 10 ga watan Maris na 2022  domin yin nazarin kotun.


0 Response to "Yanzu-Yanzu:- Abdulmalik Tanko yasake Shiga cikin Bala'i, Yayiwa Jami'an tsaro karya."

Post a Comment