--
Subahanallah😭:- Ansami Wani Dan Iska Yayiwa Matar Liman Ciki...Innalillahi wainna ilaihirrajuun

Subahanallah😭:- Ansami Wani Dan Iska Yayiwa Matar Liman Ciki...Innalillahi wainna ilaihirrajuun

>


 Limamin wani masallaci a Jihar Oyo ya kai karar wani mamu a masallacin kotu yana zargin mamun da yi wa matarsa ciki.


Limamin mai suna Alhaji Lukman Shittu ya kai kara ne a kotun gargajiya da ke zamanta a unguwar Mapo da ke Ibadan, babban Jihar Oyo.jaridar Aminiya trust na ruwaito

Liman Lukman Shittu, ya ce “Abin mamakin shi ne mutumin da ya mayar da Fisayo (matar limamin) sa-dakarsa yana bi na sallah a masallacin da nake jagoranta?”

Malamin ya zargi matar tasa da kwartanci ne bayan matar ta yi karar shi a gaban kotun tana neman rabuwa da shi.


A masallacina kwartonta ke sallah


A cewarsa, ta hanyar bin mazan da take yi ne ta haifi ’ya’ya uku da suke rikici a kansu.

Tun da farko Shittu ya shaida wa kotun cewa bayan matar tasa ta kwashe kayanta daga gidansa a 2021 ta fara tuka wata dalleliyar mota.

“Fisayo ta rika burga cewa wani dan uwanta ne ya ba ta motar, amma a bincikena na gano cewa kwartonta da suka dade tare ne ya saya mata motar.

“Ya Mai Girma, Fisayo ta fara rawar kai ne tun wani lokaci da na kasa ba ta kudin kama hayar shago.

“Daga lokacin ta daina dawowa gida da wuri har na yi mata kashedi cewa idan ta kara, to zan kulle gida in bar ta a waje, amma maimakon ta daina, sai kawai ta kwashe kayanta ta bar gidan tare da yaran su uku.

“Ta sauya wa karamin makaranta ba tare da na sani ba, sauran biyun kuma suka ce su ba za su kara dauka ta a matsayin mahaifinsu ba.

“A watan Ramadan da ya gabata na bukaci na tsakiyan ya dawo wurina da zama, amma ya ki; Shi kuma babban, da aka ba su hutu a makaranta, kin zuwa wurina ya yi.

“Abin mamaki shi ne mutumin da ya mayar da Fisayo sa-dakarsa mamu ne a masallacin da nake jagoranta?”

Mutumin banza ne

Da take nata jawabin, matar mai suna, ta ce mijin nata ba shi da dattaku, kuma “Shittu ya yaudare ni na karbo rance daga wani karamin banki bisa alkawarin ni ce zan yi amfani da kudin in fara sana’a amma ya ki biya.

“A yunkurinsa na cimma manufarsa, har barazanar caka min wuka ya yi min, idan ban tattara kayana na bar mishi gidansa ba. Ga shi kuma mutum ne mai yawan zuwa da matan banza gidan aurenmu.

“Ya rusa shagon da na gina da kudina na sa kaya a ciki, duk a yunkurinsa na hana ni samun damar yin sana’a.

“Yana yawan zagi na, har yakan nesanta kansa da alhakin daukar nauyina da na yaran.

“Duk da cewa ’yan uwansa na dangin uwa da uba sun sa baki, dole na kwashe kayana domin in tsira da rayuwa ta,” a cewarsa.


A je a yi gwajin DNA —Kotu


Bayan sauraron bayanan kowane bangare, shugaban kotun, S. M. Akintayo, ya umarci ma’auratan da su je asibiti a yi musu gwajin kwayar halitta ta DNA tare da ’ya’yan nasu domin tantance asalin mahaifin yaran.

Shugaban kotun ya ce: “Shittu da Fisayo ne za su dauki nauyin gwajin na DNA, kuma za a kawo sakamakon gwajin kai-tsaye ba tare da an bude ba zuwa ofishin rajistaran kotun.”

Daga nan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Mayu domin a kawo sakamakon gwajin na DNA

0 Response to "Subahanallah😭:- Ansami Wani Dan Iska Yayiwa Matar Liman Ciki...Innalillahi wainna ilaihirrajuun"

Post a Comment