--
Da Dumi-Dumi- Wani Furodusa yayi wuff da Jamila Nagudu, An kusa shan biki

Da Dumi-Dumi- Wani Furodusa yayi wuff da Jamila Nagudu, An kusa shan biki

>


 Da Dumi-Dumi- Wani Furodusa yayi wuff da Jamila Nagudu, An kusa shan biki


Fitacciyar Jaruma masana’antar shirya fina-finai ta hausa Jamila Umar Nagudu, Jamila Nagudu na daya daga cikin jarumai mata da suka ga jiya suka ga yau, an dade ana damawa da su.


Jamila Nagudu na daya daga cikin jaruman da suka karbe kambun karamawa ba adadi, ga tarin masoya da Allah ya bata a ko ina a fadin duniya.


Duk da cewa jarumar tana yaro amma hakan be hana ta yin sana’arta ta fitowa da shirya fina-finai ba.


Kuma alumma suna yabon ta da irin jajircewa da kokarin neman nata da ta keyi.


A safiyar yau ne, 19 maris 2022, wani hoton Jarumar cikin yanayi hotunan kafin aure, da ita da furodusa Abdullahi Abbas.


Abokan sana’arta da dama sun daura wannan hotunan a shafukan sada zumunta, wanda ake ganin cewa Abdullahi Abbas yayi wuff da Jamila Nagudu


Sai dai haryanzun ba wata majiya da ta sanar cewar aure zasuyi, mun kira jarumar a waya bamu same ta ba domin jin karin bayani.


Zamu zanta da maku santa jarumar domin muji gaskiyar batun, shin wani film ne ko talla ake shiryawa, ko kuma auren ne zasuyi da gaske.

0 Response to "Da Dumi-Dumi- Wani Furodusa yayi wuff da Jamila Nagudu, An kusa shan biki"

Post a Comment