--
YANZU-YANZU: Gobara ta tashi a Hedikwatar Ma'aikatar kudi ta Nijeriya dake Abuja.

YANZU-YANZU: Gobara ta tashi a Hedikwatar Ma'aikatar kudi ta Nijeriya dake Abuja.

>

Gobara ta tashi a hedikwatar ma'aikatar kuɗi ta Najeriya da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Babu tabbaci kan ko me ya jawo gobarar sai dai tuni ma'aikatan kashe gobara suka isa wurin.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito mai magana da yawun hukumar kashe gobara wato Abraham Paul inda ya ce ma'aikatansu na can suna ƙoƙarin kashe wutar.

A wani saƙo da ma'aikatar kuɗi da kasafi ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce gobarar ba ta yi muni ba kamar yadda aka yi ta zuzutawa a shafukan sada zumunta inda ta ce wasu batira ne da aka keɓe suka kama da wuta a wani zaure da ke ƙasa a cikin hedikwatar ma'aikatar.



0 Response to "YANZU-YANZU: Gobara ta tashi a Hedikwatar Ma'aikatar kudi ta Nijeriya dake Abuja."

Post a Comment