--
Mafi karancin albashin da ma’aikata zasu karba shi ne dubu 30 - Gwamnan Kogi

Mafi karancin albashin da ma’aikata zasu karba shi ne dubu 30 - Gwamnan Kogi

>

 Gwamnatin jihar Kogi ta amince da aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 30,000 ga ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi.

Gwamnatin jihar ta amince da aiwatar da sabon tsarin albashi ga ma’aikatan jihar nan take, tare da gyara wani bangare na tsarin.


Sakatariyar gwamnatin jihar Folashade Arike Ayoade ce ta bayyana hakan bayan wata tattaunawa mai zurfi da shugabannin kungiyar kwadago a Lokoja.


Ta ce jinkirin da aka samu wajen aiwatar da shi ya samo asali ne sakamakon gazawar kwamitin da aka dorawa alhakin kula da shirin na yin taro akai-akai sakamakon annobar COVID-19 da ta mamaye duniya.


Madam Ayoade ta yabawa kungiyar kwadago bisa fahimta da hakurin da ta yi a duk lokacin da aka dauka kafin aiwatar da sabon tsarin mafi karancin albashin.


A halin da ake ciki, shugabar ma’aikatan jihar, Hannah Odiyo, ta ce tare da sanya hannu kan yarjejeniyar sabon mafi karancin albashi na kasa, kwamitin ya kammala aikinsa cikin kwanciyar hankali ba tare da yajin aikin ba.


Hakazalika, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC na jihar, Kwamared Onuh Edoka, ya ce ma’aikatan jihar sun zama daya da takwarorinsu na sauran Jihohin da tuni suka fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi, ta hanyar sabon tsarin albashi da aka amince dashi.


Kwamared Edoka ya kara da cewa da rattaba hannu kan dokar sabon mafi karancin albashin, yanzu sun dakatar da yajin aikin da shirya yi a baya ba tare da bata lokaci ba.


0 Response to "Mafi karancin albashin da ma’aikata zasu karba shi ne dubu 30 - Gwamnan Kogi"

Post a Comment