--
Ku maida hankali akan kwarewa fiye da satifiket, Fantami ya gargadi matasa

Ku maida hankali akan kwarewa fiye da satifiket, Fantami ya gargadi matasa

>

 


Ministan harkokin sadarwa na kasa Nigeria, Sheik Isa Ali Fantami, ya gargadi matasan Nigeria, kan cewa su zama gwanaye ta fannonin kwarewa daban-daban, fiye da takardar shaida, wanda matukar suka kasance haka, to matsalolin Nigeria zasu zama tarihi da yardar Allah. 

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa, Ministan ya faɗi haka ne a wurin taron miƙa kyauta ga waɗanda suka samu nasara a gasar National Talent Hunt Challenge a jihar Katsina.

Hakan na zuwa kwana guda da kungiyar malaman jami'oi ta kasa ASUU tace shaidar matakin zama shehin malamin boko (Farfesa) da wata jami'a ta baiwa ministan ba daidai bane, saboda bai cancanta ba a cewarsu, kuma zasu hukunta jami'ar da ta bashi. 

0 Response to "Ku maida hankali akan kwarewa fiye da satifiket, Fantami ya gargadi matasa"

Post a Comment