Saboda Ina Son Kotu Tayi Adalci Irin Nata Shi Yasa Ban Musanta Kashe Hanifa Ba, Cewar Abdulmalik Tanko
Wednesday 26 January 2022
Comment
Saboda Ina Son Kotu Tayi Adalci Irin Nata Shi Yasa Ban Musanta Kashe Hanifa Ba, Cewar Abdulmalik Tanko
Cikin wata gajeruwar tattaunawa da sashen Hausa na VOA yayi da shi, wanda ya tabbatarwa da jami'an tsaro da kansa cewar shine wanda ya kashe Hanifa, Abdulmalik Tanko ya bayyana cewar bai yi amfani da wuƙa ko wani makami ba wajen daddatsa jikin Hanifa kamar yadda ake faɗa.
Tanko ya bayyana cewar, abinda yasa bai musanta cewar shine ya kashe yarinyar ba, saboda yana so ne kotu tayi adalci irin nata.
Kazalika Tanko ya bayyana cewar, "Dama nayi niyar bayyana kaina koda ba'a kama ni ba, sakamakon yadda abin yake damuna." Inji shi
0 Response to "Saboda Ina Son Kotu Tayi Adalci Irin Nata Shi Yasa Ban Musanta Kashe Hanifa Ba, Cewar Abdulmalik Tanko"
Post a Comment