--
Hanyar da zakubi domin hana wayarku ta Hannu Android Daukan Zafi (Dumi)

Hanyar da zakubi domin hana wayarku ta Hannu Android Daukan Zafi (Dumi)

>

Wani abu da ya ke yawan damun masu amfani da wayoyin hannu musamman irin wadannan wayoyin komai da ruwanki wato Smartphones shi ne yawan yin zafi kamar zata kona hannu ko kuma dimi da mutum bai samun kwanciyar hankali da shi. Wani lokaci ga maza sai su ce idan suka saka ta a cikin aljihunsu sai ta dau zafi, wani lokaci ma sai ka dauko ka duba kawai sai ka ga ai ta mutu saboda da irin wannan zafi.

A wannan darasi da zamu yi zamu fada muku abubuwan da ke kawo

waya ta rika yin zafi da kuma hanyoyin da zamu kiyaye domin mu hana ita wannan wayar yin zafi.

Masu yawan sauraron labarai sun sami labarin kiranye da janye wayar kamfanin Samsong suka yi a ‘yan kwanakin baya kasancewar sabuwar wayar data shigo kasuwa haka nan kawai sai ta kama da wuta saboda matsala da aka samu wurin gina batirin ta. Wannan ya sanya muka ga ya dace muyi muku bayani game da irin zafin da idan kaji wayarka tana yi ka gane cewar akwai matsala.

Waya Na Yin Dumi

Baki ko sabon shigar amfani da wayoyin smartphone su sani cewar irin wannan wayar tana yi dumi wanda ya sha banban da irin kananan wayoyin da suke amfani da su a baya. Mu sani smartphones kayan wutan lantarki ne, saboda haka don kaji tayi dumi ka sani ba wani matsala ba ne.
Amma kuma idan kaji tayi zafi wanda kake jin tsoron zai iya lalata ta, ko kuma ta yi zafin da kake jin tsoron za ta iya fashewa ko ma ta la’anta masu amfani da ita to lallai ka na inda ya dace, domin abin da zamu tattauna ke nan.
Duk da cewar mafi yawan abin da zan fada sun fi karfi ga wayoyi masu amfani da tsari na Android domin kusan su aka fi amfani da su a wannan nahiya tamu ta Afirka musamman Najeriya ta Arewa.

Ta wane wuri waya ke yin zafi?

Abu na farko da ya kamata mu fara kiyayewa shi ne ta wani wuri wayar take fara yin zafi? Duk da cewar nasan ba kuwa ba ne zai iya lura ko kiyayewa ba, amma dai zai iya yiwuwa ta batir ne ko kuma cajar wayar ita take haifarwa.
To amma bari mu mu fadi wuraren da waya zata iya daukar zafi ko kuma ta inda ake iya gane cewar waya tana zafi ba dumi ba.

Bayan wayar ke yin zafi

Duk lokacin da ka ji wayarka idan zata yi zafi ba inda yake yin zafi sai bayan wayar wato inda batirinta yake to ka sani ba wayar bace ke da matsala batirin wayar shine ke kawo zafi a wayar. To idan ka tabbatar da haka ka samo wani batiri irin nata a saka a gwada idan ka ji wannan batirin baya zafi to sai ka je ka sayo wani sabo ka canza.

Zafin ta kasan wurin caji ne

Wani lokaci zaka samu wayar bata yin zafi ko fara yin dumi sai bayan ka saka ta a jikin wuta domin yi mata caji, wannan matsalar tafi faruwa a lokacin da mutum ya ke amfani da wata cajar da ba ta asalin da wayar ta zo da shi ba. Domin mutane da yawa basa fahimtar cewar ba kowane irin caja ba ce ke yiwa kowace irin waya caji koda kuwa bakin su iri daya ne ko da kuwa kamfani daya ne da wayar mutukar ba irin na wayar bane.
Ita waya tana karbar wuta ne wanda aka salantar da ita wato DC, shi kuwa wannan DC din karfi karfi ne, domin kowace waya tana da naka karfin wutar da ake son ya caza ta. Shi yasa zaka samu wata wayar idan aka aro mata caja sai yayi awanni bai iya cajin wayarba, wani kuma cikin dan kankanin lokaci sai ya cika maka wayar ka. To wannan matsalace sosai domin yin amfani da cajar wayar da yake sata tayi caji da wuri yana bata batir shi kanshi ga kuma bata injin da yake lura da karfin shigar wuta a cikin wayar.

To wannan yake nuna mama cewar idan muka tsinci wayarmu na yin zafi daga bakin caja mu sami wata caja irin ta wayar ko muce follow come kamar muke fadi idan muka gwada muka ga bata zafin ko dimi to kunga mun gane matsala, idan kuwa muka gawa muka ga har yanzu dai tana zafi ya nuna kodai batir din shi ke dawo da wutar da ke shiga cikinsa, ko kuma daga charging point ne.

Yin zafi ta baya amma saman batiri
Idan kuma ka duba kaga wayar tana yin zafi ta baya amma kuma sai ka lura da cewar ba daga wurin zaman batirin ba ne to zai iya yuwuwa ita karan kanta wayar ce ke yin zafi. Idan kuwa haka ne to bari in da lissafo wasu wuraren da zamu taba ko lura domin mu gane ta ina zafin ke farawa?

Wayar na zafi ta wurin sauraron magana (Speaker)
Wani lokaci za ka ji idan kana waya sai kaji kunnen ka ya dau zafi ta wurin speaker to irin wannan matalar ba wai zafi da konewar kunnan naka a ke ji ba wannan zafi zai iya shafar lafiyar kwakwalwarka saboda haka idan ka ji duk lokacin da ka ke amsa waya kunneka na zafi to ka canza wayar ko kuma na nemi headphone mai kyau ka siya ka rika amfani da shi.

Fuskar wayar ke yin zafi Screen?
Wani lokaci zaka samu idan kana amsa waya zaka samu fuskar wayar ne ke yin zafi to idan haka na faruwa akwai abubuwa da zamu lissafo wadanda ya kamata mu yi domin hana wayar tamu yin wannan zafi ta fuska.

Boyayyun Abubuwan da ke sa waya yin zafi
Tun da mun fado wadansu hanyoyi da ake iya gane waya na yin zafi a zahiri, to bari mu fado wadansu abubuwa da suke sanya ita wayar ta rika yin zafi wanda ba kasafai mutane suke fahimta ba.

Application da yawa suna aiki lokaci guda
Wani lokaci ba wadancan abubuwan da muka lissafo su suke sa yawa ta rika yin zafi kodawane lokaci ba, yawan kunna application na wayar da kuma barinsu a kunne kodawane lokaci shima yana sa waya ta rika yin zafi. Saboda haka yake da kyau duk lokacin da mutum yaji wayarsa na yawan yin zafi ya rike bude Application Manager din sa yana gobe budaddun application wannan zai taimaka masa sosai.

Akwa wadansu application na musaman wadanda suke yin irin wannan aiki kodayake suna da tasu matsalar suma amma dai mu sami application da yake irin wannan aikin domin taimakawa wayar ta mu.

Abu mai nauyi da tsawo da cin lokaci
Ba mai shakkar cewar wayoyin Android akwai dadi wurin yin amfani da su musamman idan muka yi la’akari da irin abubuwan da ake iya yi da su, kamar daura musu bidiyo mai nauyi, ko kuma kallon bidiyo mai tsawo, ko daura game mai nauyi da kuma amfani da shi, ga sauraron sauti na karatu ku nishadi, ga yadda muke shiga intanet da duba imel da dai makamantansu dukkansu kuma akan wannan ‘yar karamar wayar da bata wuce ta zauna a tafin hannunka ba.

Saboda haka mu sani kallo ko sauraron abu mai nauyi zai iya sanya waya tayi zafi musamman idan tana rike a hannunmu ne domin ka zafin hannu ga na riko ga kuma nata zafin na kanta, saboda haka yaka da kyau mu guji matsawa wayoyin mu da kallon bidiyo masu tsawo kuma buga game masu nauyi musamman irin wadanda suke bukatar higher configuration wurin amfani da su ko kuma daura su a jikin wayoyinmu.

0 Response to "Hanyar da zakubi domin hana wayarku ta Hannu Android Daukan Zafi (Dumi)"

Post a Comment