--
Jama'a a kara kulawa sosai da 'Yan damfarar Yanar Gizo Suna turawa mutane wannan Sakon su cucesu

Jama'a a kara kulawa sosai da 'Yan damfarar Yanar Gizo Suna turawa mutane wannan Sakon su cucesu

>

 


Yauma karku gaji damu jama'a domin munayin wannan ne domin tseratar da Al-ummar mu daga fada hannun miyagun mutane masu damfara a yanar gizo wato frundster wadanda akafi sani da yahoo boys,  


Sun kirkiri hanyoyi dayawa wajen cutar mutane ta kowacce hanya wanda abaya suna kiran mutane ne tawaya sucewa su tura muau OTP yanzu kuma sun koma samar da shafin bayar da tallafi suna fakewa da haka suna cutar mutane, 


Yau munzabi yin magane ne akan wani Shafi da suka kirkira mai suna (NAFE) shi wannan shafin sun samar dashi ne domin su fake da tallafin gwamnatin tarayya,  bayan kayi Rijister dasu Zasu tura maka wancan sakon dake jikin hoton dake sama, 


Saisu buqaci katura Musu da BVN naka Da NIN naka Da Kuma N1000, maganar gaskiya babu wannan tsarin na NAFE A Tsarin Gwamnatin Tarayya,  Kwata Kwata" 


Kuma Duk Wanda Ya Aika Musu Abinda Aka Buqata Wallahi Zaiyi Kuka Domin Macutane Na Gaske muna Fatan Zakuyi Share Na Wannan Sakon Zuwaga Sauran Mutanan Mu Hausawa Domn Gujewa Fada Tarkon Wadan nan mutanen, 


Allah Ya Shig Tsakanin Nagari Da Mugu Ameen 


Kucigaba Da Kasancewa Da Shafinmu Na Bz News 24/7

0 Response to "Jama'a a kara kulawa sosai da 'Yan damfarar Yanar Gizo Suna turawa mutane wannan Sakon su cucesu"

Post a Comment