--
Cikakken bayani Game da Sakon da MTN Suka turawa Mutane

Cikakken bayani Game da Sakon da MTN Suka turawa Mutane

>





Kamfanin sadarwa na MTN ya raba wa kwastamominsa katin waya da data kyauta a matsayin diyya sakamakon matsalar da ya samu a makon da ya gabata.


Shugaban kamfanin MTN ne Karl Toriola ya tura wa masu amfani da MTN saƙon a ranar Lahadi tare da wani adireshin YouTube inda ya nemi afuwa kan katsewar sadarwa da ya samu.



Sakon na cewa “an dawo maka da katinka na waya da kuma data da ka yi amfani tsakanin 12 zuwa 7 na yamma a ranar Asabar.


Hakan na nufin kudin da mutum ya kashe tsakanin 12 na rana zuwa 7 na yamma a ranar Asabar MTN ya dawo masa da su.


A cikin sakon, shugaban MTN ya ce injiniyoyin kamfanin sun fahimci cewa an samu matsalar ne daga wata tangardar na’ura da ta mayar da kwastamomi daga tsarin 4G zuwa 3G wanda ya haifar da katsewar layukan na MTN.


Ya ce yanzu an magance matsalar.

0 Response to "Cikakken bayani Game da Sakon da MTN Suka turawa Mutane"

Post a Comment