--
wani hamshaƙin ɗan kasuwa ya yiwa ƴar shekara 14 ciki a Kano Duba yadda abun ya faru

wani hamshaƙin ɗan kasuwa ya yiwa ƴar shekara 14 ciki a Kano Duba yadda abun ya faru

>


Wani ɗan kasuwa mazaunin unguwar Agadasawa a Kano, Alhaji Ibrahim ya yi wa ɗiyar makwabcinsa ciki, mai suna Humaira Hussaini ƴar aji uku a ƙaramar Sakandare (JSS3).


Mujallar Neptune Prime ta ruwaito zantawarta da yarinyar Humaira Hussaini a Kanon kuma shaida mata yanda lamarin ya faru da cewa: “Alhaji Ibrahim ya ƙira ni zuwa gidansa wata rana bisa dalilin cewa yana son ya aike ni amma lokacin da na shiga gidan, sai na gano iyalinsa ba sa gida. Ya kulle ƙofar gida  ya ba ni lemon sha kuma ya yi barazanar cewa idan ban sha ba, zai kashe ni.


“Na karɓi lemon, bayan na shanye sai kasala ta kamani shi kuma Alhaji Ibrahim ya yi min fyaɗe”.


Humaira ta ƙara da cewa tun daga wannan lokacin, sau ɗaya kawai ta ga jinin al’adar ta, kuma bayan wasu watanni ta sanar da   mahaifinta, Hussaini Ado abin da ke faruwa shi kuwa ya kai ta asibiti. A asibitin, aka umarci mahaifin nata da ya je ya shirya kayan haihuwa domin ta fara naƙuda tana gab da haihuwa.


Mahaifiyar yarinyar, Hajiya Rafa’atu Hussaini ta shaida wa majiyar mu cewa ba ta taba zargin cewa ‘yarta na ɗauke da juna biyu ba har sai da ta haifi jaririn, kuma ta tabbatar musu da cewa makwabcinsu, Alhaji Ibrahim ne ya yi mata.


Sai dai a lokacin da aka tinkari Alhaji Ibrahim da wannan batu, ya nemi da aje a yi gwajin ƙwayar halitta na DNA, wanda bayan an yi likitan ya tabbatar da cewa lallai jaririn nasa ne amma bai yadda ba ya sake neman a sake zuwa wani asibitin a yi.


Tuni dai aka shigar da ƙara ofishin ƴan sanda amma har yanzu iyayen yarinyar sun sanar da kasa gane inda lamarin ya dosa domin suna zargin ɗan kasuwan na so ya yi amfani da dukiyarsa wajen shashantar da shari’ar.


Iyayen Humaira sun nemi agajin ƙungiyoyin Kare Haƙƙin Biladama da ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumar Hisba ta Kano da Lauyoyi da ƴan jaridu da su shiga cikin wannan lamari.


Source: Hausa Daily Times

0 Response to "wani hamshaƙin ɗan kasuwa ya yiwa ƴar shekara 14 ciki a Kano Duba yadda abun ya faru"

Post a Comment