--
Yanzu yanzu: Hankula sun fara tashi yayin da rikici ya fara kamari a yankin Ojota na jihar Legas

Yanzu yanzu: Hankula sun fara tashi yayin da rikici ya fara kamari a yankin Ojota na jihar Legas

>


An gano cewa masu zanga-zangar kafa kasar Yarabawa sun bijirewa umarnin 'yan sanda Tuni jama'a suka fara gudun ceton ransu yayin da 'yan sanda ke watsa barkonon tsohuwa da kama wasu 


Rikici ya rincabe a yankin Ojota na jihar Legas yayin da masu zanga-zangar kafa kasar Yarabawa suka bijirewa umarnin 'yan sanda suka fara zanga-zanga. 


Duk da 'yan sanda da sojoji sun mamaye wurin zanga-zangar a sa'o'in farko na yau Asabar, masu zanga-zangar daga bisani sun tsinkayi wurin, Daily Trust ta ruwaito. 


Amma kuma jami'an tsaro dauke da bindigogi sun yi kokarin hana su zanga-zangar. 


Hakan ya janyo barazana ga zaman lafiyan yankin yayin da jama'a suka fara gudun ceton rai kuma 'yan sanda suka dinga watsa barkonon tsohuwa. 


'Yan kasuwa masu tarin yawa sun rufe shagunansu domin gudun su fada lamarin kuma su tafka muguwar asara. Kamar yadda Daily Trust ta gani, wasu 'yan sanda sun fara kama wasu daga cikin masu zang-zangar.


Karin bayani na nan tafe... 


Source: Legit

0 Response to "Yanzu yanzu: Hankula sun fara tashi yayin da rikici ya fara kamari a yankin Ojota na jihar Legas"

Post a Comment