--
Wata Mata Ta Yanke Mazakutar Mijinta Ta Soya Duba Dalili>>>

Wata Mata Ta Yanke Mazakutar Mijinta Ta Soya Duba Dalili>>>

>


An kama wata mata mai suna Dayane Cristina Rodrigues Machado bisa zargin kashe mijinta tare da yanke mazakutarsa ta soya.


Matar mai shekara 33, an kama ta ne a garin Sao Goncalo na kasar Brazil a ranar 7 ga Yunin bana bayan gano gawar mijinta mai suna Andre.


An kira ’yan sanda zuwa gidan ma’auratan a Unguwar Santa Catarina kuma sun iske gawar tsirara an yanke wasu bangarori na jikinsa.


Ana dai tuhumar matar kan zargin yanke mazakutar mijin nata kuma ta soya bayan ta kashe shi da misalin karfe 4:00 na dare.


’Yan sanda sun samu wuka a wurin da ake zargin ta aikata kisan, inda alamu suka nuna cewa, ita ce ta kashe mijin ta kuma yanke wasu sassan jikinsa.


An kama Machado a wurin kuma tun daga lokacin aka zarge ta da kisan kai da kuma baddala gawa.


A cewar kafar labarai ta UOL, ma’auratan sun fita zuwa gidan cin abinci a daren da aka aikata kisan, sai rikici ya barke a tsakaninsu, 


’Yar uwar Andre, mai suna Adriana Santos, ta bayyana wa kafafen labarai cewa, wadda ake zargin ta kashe dan uwan nata.


Duk da haka, lauyan Machado, mai suna Carla Policarpo ya ce, Andre yana yi wa matarsa barazana kuma hakan ya sa ta kashe shi don kare kanta.


Kuma tun daga lokacin ne danginsu suka bayyana cewa ma’auratan suna yawan fada a tsakaninsu, kuma Machado ta kai karar mijinta ga ’yan sanda a wani lokaci.


Rahotanni sun bayyana cewa ma’auratan sun kasance tare na tsawon shekara 10 kuma suna da da mai shekara takwas da ’yarsu mai shekara biyar.

0 Response to "Wata Mata Ta Yanke Mazakutar Mijinta Ta Soya Duba Dalili>>> "

Post a Comment