--
Ta Haramta Wa ’Yan Uwanta Halartar Jana’izarta Duba dalilinta>>>

Ta Haramta Wa ’Yan Uwanta Halartar Jana’izarta Duba dalilinta>>>

>


Wata mata mai suna Maria Paz Fuentes Fernandez ta haramta wa ’yan uwanta halartar jana’izarta koda bayan ta mutu.


Matar ta ce baki 15 da ta lissafa ne kadai suke da izinin halartar bikin jana’izarta.


Kafar labarai ta Metro. co.uk, ta bayyana cewa, Maria ta sanar da haka ne a cikin wata wasiyyarta.


A wata wasika da ta rubuta da aka wallafa a birnin Lugo, a yankin Galicia na kasar Spain, matar ta fitar da jerin sunayen baki 15 da za su halarci jana’izarta.


Maria ta bayyana cewa, danginta sun nesanta kansu da ita kuma ba su kula da ita ba na tsawon lokaci.


Dalilin haka ne ya sanya ta ce a ganinta babu bukatar sai ’yan uwanta sun halarci jana’izarta.


“Tunda ’yan uwana na jini ba su tare da ni na tsawon lokaci don haka na fitar da wasiyyata ta karshe.


“Mutanen da na lissafo ne kadai za su iya halartar jana’izata, ko a harabar wurin jana’izar da za a yi a coci ko makabarta.


“Ga duk wanda bai taba kula da rayuwata ba, ya fita sabgata, kamar yadda kuke yi a da kafin rasuwata,” a cewarta.Wasikar da Maria ta zayyana sunaye wadanda kadai za su halarci jana’izarta

0 Response to "Ta Haramta Wa ’Yan Uwanta Halartar Jana’izarta Duba dalilinta>>>"

Post a Comment