--
Duba Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka a halin yanzu

Duba Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka a halin yanzu

>


Akalla ma'aikatun gwamnatin tarayya uku ne ke shirin daukar ma'aikata a wannan shekarar, wadanda suka hada hukumar sojin kasa ta Najeriya, sojin sama da hukumar kula hadurran kan hanya ta kasa wato FRSC. 


Don tabbatar da 'yan Najeriya masu sha'awar neman ayyukan ba su fada hannun 'yan damfara ba, wannan ya rubutu ya bayyana hanyoyin da ake wajen neman aikin cikin sauki.


Sojin kasa na Najeriya Hukumar sojin Najeriya na karbar takardun neman aiki na 'Regular Recruit Intake 81'. Don kauce wa zamba, hukumar tsaro ta saukaka lamarin ta hanyar samar da cibiyoyin daukar ma'aikata na zahiri a dukkan jihohi 36 na tarayyar da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT). 


An fara daukar ma’aikatan ne a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, kuma za a rufe a ranar Asabar, 24 ga watan Yuli, a cewar rundunar. 


Ga mai sha'awa, ga jerin dukkan cibiyoyin daukar ma'aikatan da aka samar: Sojin Sama na Najeriya Hakanan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) tana neman wadanda suka kammala karatunsu na digiri da wadanda suka kammala karatunsu na digirgir domin a horar da su a matsayin 'Cadets Service Short Cadets'. 


Za a bude kafar yanar gizo ta aika takardun neman aikin a ranar Litinin, 26 ga Yuli, kuma za a rufe ta Litinin, Agusta 30. Ga masu sha'awar neman wannan aikin, ba kwa bukatar ziyartar kowane dandamali na kafofin sada zumunta. 


Abinda ya kamata kuyi shine ka ziyarci kafar yanar gizo ta NAF. Hakanan masu sha'awar neman za su iya kiran wadannan layukan domin agaza musu a inda suka shige duhu daga 9:30 na safe zuwa 5:30 na yamma, 


Litinin zuwa Juma'a, 09064432351, 08043440802, 09055840142 ko Email: caeers@airforce.mil.ng idan ana bukatar karin bayani. Dole ne su kuma lura cewa kyauta ne cika wannan aiki. Ga mai bukata, dole ne ka kasance dan asalin Najeriya. 


Dole ne ka kasance tsakanin shekarun 20 zuwa 30 kafin 30 ga Satumba 2022. Wadanda ke neman matsayi a harkar likitocin gidan soji, dole ne su kasance tsakanin shekaru 25 - 40. 


Danna nan ko a nan don cikakken jerin abubuwan da ake bukata don neman aikin. Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) Hakanan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) tana daukar ma'aikata musamman ga mukamai uku: 


Officer cadre Marshal inspectorate (MI) cadre Road marshal assistant cadre Don neman wannan aiki, ziyarci kafar yanar gizo ta FRSC, www.recruitment.frsc.gov.ng


Ana sa ran masu neman mukamin 'Officer cadre' su mallaki digiri na farko, takardar shaidar kammala NYSC, kuma dole ne su zama basu wuce shekaru 30 ba. Danna nan don samun cikakken jerin abubuwan da ake bukata don neman aikin. Source: Legit

0 Response to "Duba Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka a halin yanzu "

Post a Comment