--
DA DUMI-DUMI: Mahajjatan shekarar 2024 za su biya Naira Miliyan hudu da rabi

DA DUMI-DUMI: Mahajjatan shekarar 2024 za su biya Naira Miliyan hudu da rabi

>

DA DUMI-DUMI: Mahajjatan shekarar 2024 za su biya Naira Miliyan hudu da rabi 

DAGA Comr Abba Sani Pantami

Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bukaci hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, da su karbi Naira miliyan hudu da rabi 4.5 a matsayin kudin aikin Hajji na shekarar 2024.

Hukumar ta ce farashin aikin hajjin 2023 ta karbi Naira miliyan 2.8, inda a lokacin farashin Dala tana Naira 450.

A yanzu kuma Dala tana kan Naira 750 ko sama da hakan, wanda ya zama dole kudin ya kusan linkawa saboda da Dala suke amfani wurin hada-hadar komi. 

Muna Addu'ar Allah ya hore mana, ya bamu ikon biya.✍️✍️

CREDIT. Legit Ng Hausa. 

0 Response to "DA DUMI-DUMI: Mahajjatan shekarar 2024 za su biya Naira Miliyan hudu da rabi"

Post a Comment