--
ABIN A YABA: Hukumar Gidan Yarin Kurmawa Dakè Jíhar Kanó Ta Aika Da Takardar Yabo Da Godiya Ga A'isha Humaira

ABIN A YABA: Hukumar Gidan Yarin Kurmawa Dakè Jíhar Kanó Ta Aika Da Takardar Yabo Da Godiya Ga A'isha Humaira

>

 ABIN A YABA: Hukumar Gidan Yarin Kurmawa Dakè Jíhar Kanó Ta Aika Da Takardar Yabo Da Godiya Ga A'isha Humaira 

-Jarumar Masana'antar Kannywood, A'isha Humaira Ta Ba Da Tallafin Magunguna Da Kayayyakin Amfani A Gidan Yarin Kurmawa.

-Ko Da A Kwanakin Baya A'isha Humaira Ta Kai Ziyarar Ba Da Tallafi Gidan Yarin Tare Da Biyawa Ɗaurarru Masu Ƙananan Laifuffuka Kuɗin Tara 20,000. 30,000. 40,000. 50,000.

Hukumar gidan Yarin Kurmawa a Jihar Kano, ta aike da takardar yabo da godiya ga jarumar masana'antar Kannywood, A'isha Humaira a bisa tallafin magunguna da kayayyakin amfani da ta bayar a gidan yarin domin tallafa ɗaurarru su samu kiwon lafiya da nutsuwar zaman tare.

 ta samu bayanin hakan ta cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun mataimakin shugaban gidan, Mu'azu Tukur inda takardar ta bayyana cewa:

"A madadin hukumar wannan gidan yari na Kurmawa da ma'aikata da ɗaurarru mun yaba matuƙa da waɗannan kayayyaki na tallafi da jinƙai da ki ka bayar domin amfanin ɗaurarru". 

Kayayyakin da A'isha Humairan ta bayar kamar yadda takardar ta ƙara da cewa sun haɗa da: Magunguna, butoci da taburmi da bokitai gami da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.

Idan ba ku manta ba, ko da a kwanakin baya, Hajiya A'isha Humaira ta biyawa ɗaurarru masu ƙananan laifuffuka kuɗin tara waɗansu Naira 20,000 wasu Naira 30,000 wasu Naira 40,000 wasu kuma Naira 50,000. Wanda kuma hatta hukumar gidan yarin ta yaba tare da gode mata cikin takardar bisa wannan aiki na agaji da ta yi

CREDIT. Legit Ng Hausa. 

0 Response to "ABIN A YABA: Hukumar Gidan Yarin Kurmawa Dakè Jíhar Kanó Ta Aika Da Takardar Yabo Da Godiya Ga A'isha Humaira "

Post a Comment