--
Hatsarin da yake cikin  chanja ko saida wayar hannu ba tare da sauke Gmail account dinku akan wayar ba

Hatsarin da yake cikin chanja ko saida wayar hannu ba tare da sauke Gmail account dinku akan wayar ba

>

 Yana da kyau ga duk wanda zai chanja waya ko kuma zai yiwa wayarsa Restore, to ya sauke Gmail account ɗinsa daga kan wayarsa saboda dalilai kamar haka:

1. Idan ka chanja sabuwar waya sai ka siyar ko ka bayar da tsohuwar wayar taka ba tare da ka sauke Gmail account ɗinka daga kan wayar ba to gaskiya kayi babban kuskure, wannan Gmail ɗin naka da ka bari za a iya cutar da kai ta hanyar shiga wasu account ɗin da ka buɗe da wannan Gmail ɗin ayi amfani da shi ko kuma a kwashe maka kuɗaɗenka idan account ɗin na kuɗi ne, idan kuma social media account ne za a iya yin posting wani abu bada izininka ba ko kuma a ƙwace social media account ɗin baki ɗaya daga wajenka, a taƙaice dai barin Gmail akan wayar da ka siyar yana da illa sosai.

2. Idan kayiwa waya Restore ba tare da ka sauke Gmail ɗin dake kan wayar ba, to bayan ta gama Restore ɗin dole sai ka saka kayi Sign In na wannan Gmail ɗin dake kan wayar kafin kayi mata Restore, matsalar shine idan ka manta Password na Gmail ɗin kaga ba zaka iya Sign In ba, ko kuma dama Gmail ɗin dake kan wayar ba naka bane ba kasan Password ɗin ba, to anan shikenan wayar ba zata buɗe ba har sai anje anyi bypass na Gmail account idan an tabbatar da wayar taka ce kenan, kunga kenan idan da an sauke Gmail daga kan wayar tun kafin ayi mata Restore da hakan bai faru ba.

Don haka a kiyaye a riƙa sauke Gmail daga kan waya idan za a siyar ko kuma za ayi mata Restore. 

Kindly join our WhatsApp group to get updates regarding recruitment and different types of updates. 

https://chat.whatsapp.com/Ib66myTN1AV9AE8Zi0A4Ra

Credit. KK Techtube. 

0 Response to "Hatsarin da yake cikin chanja ko saida wayar hannu ba tare da sauke Gmail account dinku akan wayar ba "

Post a Comment